Saturday, November 26, 2016

Hudubar Jumu’a Masallacin ITN: ASARAR LOKACI


Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N Zangon-Shanu, Zaria

Daga Bakin Malam Farfesa Ibrahim Ahmed Aliyu




Asslamu Alaikum.

Bayan haka:

‘Yanuwa Musulmai, ‘lokaci’; Lokaci yana da muhimmanci, lokaci shine rayuwa, kamar yadda Hasan Al-Banna ya fada. Lokaci ya fi komai tsada, lokaci ya fi Zinari da Azurfa da Lu’u-lu’u... Wadannan abubuwa masu karewa ne, amma lokaci shine rayuwa, duk wanda ya bata lokaci, bangare na rayuwar sa ya bata. 

Laifin da ya fi kowane laifi a Musulunci shine wanda za ayi ta hanyar bata lokaci. Laifin bata lokaci yafi laifin barnar dukiya. Muna ganin Al’ummar mu tana bata lokaci a banza, lokaci ya zo, ya wuce ana wasanni. Yawancin mutane ba su yin abin da ya dace da lokaci. Da dare, wasu su zauna ba su wani abu. Da rana kuma suna zaman banza da wofi, ana hira, ana zancen banza da na sabon Allah; ana cin mutuncin mutane, ana kuma yi da su. Har wadanda ke wajena aiki ba su tsira ba. 

Saboda haka lokaci yana da matukar amfani a Musulunci, don hakane Allah ya rantse da lokaci da bangarorin lokaci kamar su Alfijir, walaha, dare, da wuni. Meyasa Allah yayi wannan rantsuwa? Saboda Allah ya nuna mana muhimmancin wannan abu. 

Lokaci kamar takobi ne, idan har kai ba ka yanke shi ba, ya yanke ka. Saboda lokaci yana aiki a kan ka, kamar yadda Umar dan Abdul Azeez ya fada. Hakika lokaci yana aiki a kan ka kai mutum, kai ma kayi aiki a cikin sa. Ma’anar suna aiki a kan ka shine suna rage maka tsawon rayuwar ka. Duk wani sabon abu, lokaci zai maida sa tsoho. Duk abin da ke nesa, lokaci zai kawo sa kusa. A kullum lokacin mu ne yake tafiya da wani bangare na rayuwar mu. Kamar yadda Hasan Al-Basri yake cewa, ya kai ‘Dan Adam, kai ba komai illa tari na lokaci, lokaci ne aka tara ya zama kai. Saboda haka duk wata rana da ta tafi, wani bangaren ka ne ya tafi. Don haka, ka da ka jinkirta aikin yanzu zuwa dare, ko kuma aikin yau zuwa gobe. Malalaci ne kawai yake yin wannan, amma Musulmai a yau sun zama masu kasala,’yan zaman kashe wando. Muna cewa da sannu zan yi kaza. 

Ka da mutum ya zama yana cewa da sannu zan yi kaza, nan gaba zan tuba…ya aka yi ka san cewa za ka rayu zuwa wannan lokaci? Wa ya lamunce maka rayuwar ta ka? An ce maka za ka rayu zuwa wannan lokaci ne bayan kana da wannan dama a yanzu? Ko waya fada maka cewa idan ka fito daga gidan ka, za ka koma? Wa ya tabbatar maka da cewa tufafin ka, kai ne za ka tube su, ba mai wankan gawa ba?  

Saboda haka ya wajaba mu yi wa kan mu hisabi, mu ga me ya dace mu cigaba da aikatawa. Magabatan Malamai su kan ce; duk wanda yau din sa ta zama kamar jiya, kamar yana ciniki ne yayi asara, wanda kuma yau din sa ta fi jiya sharri, wannan la’ananne ne. Sai mu roki Allah ya fitar da mu daga cikin masu asara da kuma la’anannu. 

Muyi kokari mu tashi tsaye, muyi aiki wurjanjen domin mu samu Aljanna da ta fi kowace. Kamar yadda aka ruwaito Manzon Allah SAW yana cewa idan za ku roki Aljanna ku roki Aljannar Firdausi. Muna rokon Allah ya azurta mu da Aljanna Firdausi. 

Ya wajaba a kan mu, a wannan tsayuwa da muka yi, a wannan lokaci, mu gane abin da ya kufce mana, wanda ba mu aikata ba. Mu san kimar lokaci, da wannan rayuwa da Allah ya mana ni’ima da ita, za a fa yi mana tambaya a game da abin nan duka a Filin Tashin Kiyama, domin ya zo a wani Hadisi Ingantacce da Bazzar da Tabarani suka ruwaito. Sai an tambayi Dan Adam, a kan me ya gudanar da rayuwar sa; samartakar sa da kuruciyar sa, dukiyar sa, da Ilmin sa. Guda biyu daga cikin su, sun shafi lokaci ne. Annabi SAW yayi wa’azi yake cewa ku ci gajiyar abubuwa 5 kafin abubuwa 5 su same ku. Ka ci gajiyar samartakar ka kafin tsufa ta same ka. Lafiya, kafin rashin lafiya ta same ka. Wadata kafin talauci ya zo maka. Kana da lokacin yin abubuwa, kayi amfani da lokacin kafin abubuwa su sha kan ka. Rayuwar ka gaba daya kafin mutuwa ta zo maka. A lokacin Samartaka ne mutum yake da karfin ikon aiki ga Musulunci. Ka da mutum ya bata kuruciyar sa. Haka lafiya babbar ni’ima ce, ya kamata mutum yayi amfani da lafiyar sa wajen aikata alheri. Haka nan kuma mutum yayi amfani da wadatar sa ta hanyar alheri kafin talauci ya zo. 

Ba ana nufin mutum ya zama yana cikin Sallah da Zikiri a kodayaushe ba, A’a gaba dayan rayuwar Addinin Musulunci, ibada ne. Amma mutane ba su san kimar rayuwa ba har sai lokacin da Mala’ikan mutuwa ya zo zai karbi rai, a lokacin ne mutum zai rika neman ina ma a jinkintar masa kamar yadda Allah SWT yayi bayani a cikin Ayoyi. Saboda haka lokaci abu ne mai tsada kwarai, abu ne mai darajar gaske, domin lokaci idan har ya tafi ba ya dawowa. Kamar yadda Hasan Al-Basri ya fada. Muna rokon Allah ya bamu ikon amfani da lokacin mu ba tare da mun yi almubazaranci ba.

  
Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Zaria.

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...