Monday, November 7, 2016

Kasar Switzerland ta karbe motocin Mataimakin Shugaban Kasar E/Guinea

Kasar Switzerland ta karbe motocin Mataimakin Shugaban Kasar Equatorial Guinea

 

Jami’an Kasar sun karbe motocin Mataimakin Shugaban Kasar na Afrika har guda 11

 

Mataimakin Shugaban Kasar dai dan Shugaban Kasar na Equatorial Guinea ne

 

Cin hanci da rashawa dai ya yabaibaye mutanen Afrika bisa dukkan alamu, ba kuma ‘Yan Kasar Najeriya ne kadai ba su son sauka daga Mulki ba da zaran sun dare, igiya ta ja su. Har wasu Kasashen na Afrika sun ganewa daura ‘Ya ‘yan su da Iyalan su kan kujerar mulki in har dai suna raye. 

 Wani abu sai Afrika; 'da da uba: Shugaban Kasa da Mataimakin sa

Yanzu haka, Kasar Switzerland ta karbe motocin Mataimakin Shugaban Kasar Equatorial Guinea, Teodorin Obiang Nguema. Mataimakin Shugaban Kasar Mista Teodorin dan Shugaba Obiang Nguema ne na Kasar na cikin sa. Yana da shekara 47 a duniya, Mahaifin sa, wanda shine Shugaban Kasar ya nada sa a matsayin mataimakin sa.


Teodorin Obiang Nguema ya zama Mataimakin uban sa ne a shekarar 2012, tun nan kuma ya shiga facaka da Dalolin kudi. Yanzu haka yana soyayya da wata mawakiya 'Yar Kasar Amurka. Kwanan na Jami’an Kasar Switzerland ta samu karbe wasu daga cikin motocin Mista Teodorin har guda 11. 

Teodorin Obiang Nguema da Ba'Amurkiyar Budurwar sa, Eve


Ciki motocin da aka karbe, har da motar dala miliyan $2.8, wanda ake ce duk duniya guda 7 kadai aka taba kerawa. Akwai irin su Buggati Veyron da Ferrari masu dan banzan tsada.

Duk Afrika dai babu Shugaban da ya kai Obiang Nguema dadewa a kan mulki, ya hau mulkin Kasar ne a shekarar 1979. Kasar mai arzikin man fetur da mutane Miliyan daya da ‘yan kai ne rak na fama da masifan talauci.





1 comment:

  1. Gaskiya shuwagabannin arewa, cin hanci da almubazaaranci da kudin mutane yayi shiga cikin jikin su.. Allah ya kawo mana karshen wannan abu.. Ameen

    ReplyDelete

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...