Dan
wasan Barcelona, Neymar za shi gidan yari?
– Shegen Dan wasan nan na Kungiyar Barcelona zai iya shiga Gidan Yari
– Neymar ya shiga matsala game da cinikin sa zuwa Barcelona shkearu 3 da suka wuce
– Dan wasan na Brazil, Neymar Jr. na iya kwashe shekaru biyu a Gidan maza
Hatsabibin matashin Dan
wasan nan na Kasar Brazil, Neymar Jr ya shiga cikin babbar matsala a halin
yanzu. Dan wasan na iya zarcewa kurkuku idan ba ayi wasa ba. Hukumar Kasar
Spain suna kira da a daure Dan wasan inji BBC.
Akwai hannun Dan wasan a
wata badakala cikin cinikin sayan sa da aka yi daga Kungiyar Santos zuwa
Kungiyar Brazil shekarun baya kadan da suka wuce. Ana dai zargin dan wasa
Neymar Jr. da Mahaifin sa da laifi.
Alkalin shari’ar, Jose
Perals ya jaddada cewa dole a kama Tsohon Shugaban Kungiyar ta Barcelona,
Sandro Rosell. Mista Rosell ne dai ya sayo Dan wasan daga Kungiyar Santos zuwa
Barcelona a shekarar 2013.
Shekaru biyu da suka wuce ne
dai dole ta sa Sandro Rosell ya sauka daga matsayin na sa saboda laifin da aka
kama sa da shi. Ana zargin rashin gaskiya wajen cinikin dan wasan Neymar da aka
saya kusan Miliyan €60.
No comments:
Post a Comment