Saturday, November 19, 2016

Hudubar Juma’a daga Mimbarin ITN-Zaria

Hudubar Juma’a daga Mimbarin ITN-Zaria



-Tambayoyin Kabari’-Daga Bakin Imam Ustaz Sa’eed Yunus.


Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah, 

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah SWT, tsira da amincin Allah su tabbata ga wanda babu Annabi bayan sa, Shugaban mu, kuma Annabin mu, farin Jakadar Allah; Annabi Muhammadu SAW, tare da iyalan sa da Sahaban sa tare da duk wadanda suka bisa da kyautatawa zuwa har Ranar karshe.
Bayan haka, ‘Yan uwa mu ji tsoron Allah. Lallai babban guzuri ga bawa shi ne tsoron Allah. Ubangiji ya fada cikin Suratul Nisa’i a Al-Kur’ani mai girma cewa: ‘Lallai mun yi wasici ga wanda muka ba littafi, da wadanda suka zo kafin ku, da ma ku kan ku da ku ji tsoron Allah’

Hudubar yau tana mana ne magana game da tambayoyin cikin kabari. Tabbas, bayan mun bar wannan duniya, za a bijiro mana da tambayoyi a cikin kabari wanda Allah ya rubuta. Hatta wanda ba a birne ba, sai anyi masa wadannan tambayoyi. 

‘Yan uwa sababi na mutuwa suna da yawa a yau, wasu mugaye su kan kashe mutum. Annabin Rahama SAW kuwa yayi gaskiya, yace karshen zamani, za a samu wasu masu kashe mutane, su wadanda suka yi kisan ba su san dalilin da ya sa suka yi ba, haka wanda aka kashe bai san abin da yayi aka kashe sa ba. Allah ka tsare mu.

‘Yan uwa babu wanda zai rasu, Musulmi ko wanin sa, face sai an dawo masa da ran sa a jikin sa daga lokacin da ‘Yanuwan sa su ka bar wurin bizne sa. Amma kai idan ka ga kabarin, sai kace ya abin zai yiwu? Allah kuwa ya tsara haka, ya kuma ba Mala’ikun nan biyu umarnin su tambayi bawa. 

Za a tambayi bawa abubuwa kamar haka: Wanene Ubangijin ka? Menene addinin ka? Wanene Annabin ka? Sannan ya ka san Allah? Bawa na kwarai zai amsa da cewa Ubangiji na shine Allah. Annabi na kuma shine Annabi Muhammad SAW. Addini na Islam kuma shine Addini na. Sai ace da shi ta ya ka gane wadannan, sai bawa yace na karanta littafin Allah, Al-Kur’ani. Na gaskata Manzon tsira SAW. Wannan Bawa ya samu cin jarabawa.

Duk wanda ya karanta Al-kur’ani, Ubangiji yana cewa: ‘Ubangijin ku shine Allah…’, kuma yake cewa: ‘Muhammadu SAW, manzon Allah ne…’, Sannan kuma duk wanda ya ke karatun Al-Kur’ani ya san cewa: ‘Addini a wajen Allah, shine musulunci’. A takaice, zai amsa wannan tambayoyi kuma za a bada sakamakon wannan jarrabawa da kuma kyaututtuka guda 6; Na daya; Za ayi masa shimfida da mashinfidin Aljanna. Na biyu; Za a masa tufafi da tufafin Gidan Aljanna. Na uku: Za a budewa wannan Bawa wata kofa da zai rika shakar iskar Gidan Aljanna. Za kuma a nuna masa arzikin sa na duniya. Na hudu: Za ayi masa bushara da Aljanna tun a kabari. Na biyar: Allah SWT zai yi umarni a buda ma Bawan kabarin sa, ya zama mai fadi. Na shida kuma: Ubangiji zai saka haske cikin kabarin. Wannan ya zo a cikin Hadisin Sahabi Barra’ RA a cikin Sunan Tirmidhi. 

Babban Maruwaici, Abu Hurairah RA yake cewa a wata ruwayar daga Tirmidhi. Allah kara masa yarda, cewa, Ana saka haske a cikin kabarin Bawa na gari. Sannan a cikin kabarin, Bawa zai ga wani mutum kyakkyawa mai kanshin jiki da sura  yana masa sallama da busharar isowa, ko idan bawa ya tambaye wanene wannan mai matukar kyawun sura, sai yace ni ne ayyukan ka na Gidan .
A takaice saboda wannan hadisi, sai muyi aiki mai kyau. Za a fitar da mutum daga gidan sa ana kuka, alhali yana hangen alherin da zai fuskanta gaba. ‘Yan uwa aiki ya gan mu; maza da mata. Manya da kanana. Akwai morewa ga wanda Allah ya sa suna da rabo.


Bangare na 2 na huduba

Bayan godiya ga Allah SWT da yabo ga farin jakadan Annabi Muhammad SAW. Mu ji tsoron ranar da za mu koma kabari. Mu sani cewa kabari gaskiya ne, wasu mutane sun munana ayyukan da za su gani a kabari; wasu sun zama masu ha’inci wajen aiki da sana’a. Gulma da zunde ya zama aikin wasu, wasu sun zama annamimai. Wasu suna aikata abin da Allah ya hana, wasu kuma suna yada sharri, duk wanda ya yada sharri, zai iske sharri a lahira. Jama’a suna yada cewa akwai yunwa a Kasar mu, Allah ya raba mu da yunwa. Babban Sahabi Ibn Umar RA yace: ‘Idan danuwan ku ya rasu, idan na kirki ne, zai ga farin ciki a kabarin sa. Idan kuma na banza ne, zai ga bakin ciki.’ Allah ka kare mu. 

Za ayi wa kowa wadannan tambayoyi, kamar yadda aka ambata. Idan dan wuta ne; za a yi masa tufa daga cikin kayan wuta. Za kuma a bude masa kofa daga cikin na Jahannama mai hurowa da zafi. Duhu zai cika kabarin sa har sai Ranar da aka yi busar Kiyama. Ubangiji Ta’ala SWT zai yi umarni da a kara kuntata kabarin wannan Bawa ya zama babu yalwa, daga karshe kuma ayi masa bushara da wutar Jahannama. Allah ka tsare mu. Amin. 

Don Allah me ya kamata mu zaba? Yanzu muke da rai. Babu wanda ya san abin da zai faru gare sa nan da zuwa Jumu’a ta gaba. Ya mu’amalar ka da iyalin ka? Abokan ka? Da sauran Jama’a. Allah ya sa mu dace.

Allah ka buwaiyar da Addinin Musulunci ka kaskantar da kafirci. Allah ka azurta mu, ka bamu zama lafiya a Kasar mu. Allah ka kare mu daga azabar kabari, Allah kar fitinar da mu da kabari ka tabbatar da harshen mu a cikin kabari.

[Sheikh Dr. Saeed Yunus] 


Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com           
Twitter:@Ya_waliyyi

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...