– Wasu iyaye sun saka wa ‘Dan su da suka haifa suna Donald Trump
– Mahaifin yaron yace yana matukar kaunar sabon shugaban Kasar Amurka
– Wannan abu ya faru ne a Kasar Kenya
A Kasar Kenya wani abun
al’ajabi ya faru inda wasu iyaye suka saka wa dan suka haifa sunan sabon
Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump. Wadannan iyaye sun yi sabon Shugaban Kasar
Amurka Donald Trump takawara saboda tsabar soyayya.
Jaridar Daily Nation ta
Kasar Kenya ta rahoto wannan labara. Iyayen wannan yaro sun ce Donald Trump
yana matukar burge su. Mahaifin wannan ‘da yace shi musamman akidu da
manufafofin wannan mutumi watau Donald Trump yana ba sa sha’awa kwarai da
gaske.
Mista Felix Otiano ya sakawa
dan sa da haifa kwanaki dai suna Donald Trump. An sakawa wannan yaro sunan
Donald Trump ne tun ma kafin takwarar na sa ya san zai lashe zaben
Shugaban Kasar Amurka. Mista Felix,
Mahaifin wannan ‘da yace Donald Trump ya cancanci zama Shugaban Kasar Amuka.
Wannan abu dai ya kawo
ce-ce-ku-ce a Kasar, shi dai mahaifin yace ba don ya zama Shugaban Kasa ya masa
takwara da dan cikin sa ba. Kwanakin baya, Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya
da sauran Kasashen Afrika ba za su rika samun irin taimakon da suka rika samu a
lokacin Shugaba Barrack Obama ba tun da Donald Trump ya zama sabon Shugaban
Kasar Amurka.
Donald Trump ya buge Hillary Clinton 'Yar takarar Jam'iyyar Democrat a zaben da aka kammala wancan makon na Kasar Amurka.
No comments:
Post a Comment