– Gwamnatin Shugaba Buhari za ta amince da kirkiro sababbin Jami’o’i a fadin Tarayyan Kasar
– Duk Jami’o’in da za a karo na kasuwa ne, ba na Gwamnati ba
– Gwamnatin Tarayya ta yanke wannan shawarar ne a zaman da ta yi na yau
A zaman Majalisar zartarwa
na Tarayyar Kasar watau FEC na Yau, Gwamnatin Shugaba Buhari ta amince da
kirkiro sababbin Jami’o’i a fadin Kasar nan har guda 8. Gwamnatin Shugaba
Buhari ta dauki wannan mataki ne a zaman Majalisar zartarwa na mako-mako da
tayi a Fadar Gwamnati da ke Birnin Abuja.
A taron da aka yi a Aso Rock, Gwamnatin Shugaba Buhari tayi
na’am da karo sababbin Jami’o’i guda 8 a fadin Najeriya. Sai dai kaf wadannan
Jami’o’i bana Gwamnati bane, watau na ‘yan kasuwa ne.
Shugaba Buhari ya jagoranci
wannan taro da shi da Ministocin sa tare da sauran mukarraban Gwamnatin
Tarayya. Sababbin Jami’o’in sune; Jami’ar Anchor a Legas, Jami’ar Clifford,
Jami’at Coal City, Jami’ar Dominican, Jami’ar Kola Daisi, Jami’ar Legacy dsr.
Haka kuma a yau Kungiyar
Kwadago ta Kasa watau NLC, za ta zauna da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gana da Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC, da
kuma Kungiyar ‘Yan Kasuwan Najeriya watau TUC domin ganin Shugaba Buhari ya
kara albashin ma’aikata daga N18000 zuwa akalla N56000 a kowane wata.
No comments:
Post a Comment