– Shugaban Kasa ya ce zai dauki matasa aiki amma shiru
– Shugaban Kasa yayi alkawarin daukar matasa 200, 000 aiki kafin karshen watan Jiya, amma har yau ba labari-Inji Farfesa Farouk Kperogi
Farfesa Farouk Kperogi da ke
Jami’ar Jihar Kennesaw ta Kasar Amurka ya bayyana ta shafin san a Facebook cewa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karya alkawarin da yayi. Shugaban Kasa Buhari
yayi alkawarin daukar matasa aiki kafin karshen watan Jiya, amma har an shiga
sabon wata, shiru kake ji.
Farfesa Kperogi ya nuna
damuwar sa da halin da ake ciki a mulkin Shugaba Buhari, ya kuma nuna takaicin
ga yadda matasa da dama suke zaune ba aikin yi a Kasar nan. Kwanakin baya
Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa Gwmanatin
Tarayya ta fara tantance matasa 200,000 da za ta samarwa aiki a Kasar.
Mataimakin Shugaban Kasa,
Farfesa Yemi Osinbajo ya ce zuwa karshen watan Oktoba za a samarwa matasa
200,000 aiki a Najeriya, Farfesa Kperogi yace shin ina matasan da aka samawa
aikin, ganin watan Oktoba ta kare?
Farfesa Kperogi ya bada
labarin yadda wasu dubunnai suka rasa ayyukan su a Kasar. Yace ya samu sako
daga wani cewa yana cikin mutane fiye da 1300 da aka kora daga aiki, Farfesa
Kperogi yace wannan abu akwai takaici. Farfesa Kperogi yace dole Gwamnatin
Tarayya ta zage dantse, a fara gani a kasa.
No comments:
Post a Comment