Kaji
abin da wata uwa tayi domin ta tura yaro makaranta
– Wani mutumi ya jinjinawa mahaifiyar sa da irin kokarin da tayi
– Uwar sa ta sayar da abinci na shekara da shekaru domin ganin dan ta yayi karatu
Wani
mutumi ya jinjinawa Mahaifiyar sa domin irin namijin kokarin da tayi da shi
domin yayi karatun boko. Wannan matashi yayi amfani da kafar watsa labarai na
zamani domin gudumuwar da ta ba sa a rayuwa.
Wannan
matashi mai suna Tochukwu Ebeh yace uwar sa ta aika sa Makarantar boko tun daga
Makarantar kafin firamare, zuwa Firamaren har zuwa Makarantar gaba da
Sakandare. Mahaifiyar wannan matashi ta kasance tana dafa abinci ne a gefen
titi.
Wannan
mata dai tayi shekaru 30 tana sana’ar abinci, da haka ta biyawa dan nan na ta
kudin makaranta. Tun daga Ajin Nursery har
ya kammala Sakandare inda ya rubuta jarrabawar WAEC. Wannan yaro dai yace uwar
sa ce uban sa.
A
jiya kuma wani matafiyi mai suna Abubakar Duduwule ya shirya yin tattaki tun
daga Garun Kaduna zuwa Kasar Ingila. Abubakar zai bi ta Jihar Neje ne, daga nan
sai Garin Abuja, sai ya zarce har Kasar Birtaniya, inda zai tsaya. Kuma dai zai
yi wannan tafiya ne duk a kafa.
No comments:
Post a Comment