An
taya Atiku murnar zagayowar Ranar haihuwar sa
– Tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya cika shekaru 70 da haihuwa
– Jam’iyyar APC ta taya Atiku murna, tace sune Najeriya
– Tsohon mataimakin Shugaban Kasan yayi hidima wajen inganta rayuwa da siyasar al’umma
Tsohon
mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya cika shekaru 70 a duniya, Jam’iyyar
su ta APC ta taya sa murnar wannan rana. APC tace ba zai yiwu a rubuta Tarihin
Najeriya ba tare da sunan Atiku ba.
APC
tace Atiku Abubukar ya inganta rayuwar ‘Yan Kasar nan ta fannin mu’amala, zaman
siyasa, tattalin arziki da cigaban al’umma. APC tace Atiku mutum ne wanda aba
ruwan sa da bambancin kabila ko yare.
A
sakon taya Atiku Abubakar din murnar zagayowar Ranar haihuwar sa, Jam’iyyar APC
ta roka masa karin shekaru cikin koshin lafiya da arziki, Shugaban Jam’iyyar ne
dai ya aika da wannan sako. APC tace alherin Atiku ya taba kowa a Kasar nan.
Haka
kuma dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Atiku Abubakar din murnar
zagayowar wannan rana ta haihuwar sa, Shugaba Buhari ya taya Atiku shigowa
sahun ‘Yan Saba’una irin sa.
No comments:
Post a Comment