Shekau ya fito, yace su suka kashe Abu Ali
Ni na kashe Lt. Col. Muhmmad Abu Ali-Inji Shekau
– Shugaban Bangaren Kungiyar Boko Haram, Shekau ya fito a wani sabon kaset
– Abubakar Shekau yace shi ya kashe Babban Sojin Najeriyar nan, Muhammad Abu Ali
– Shekau yace kadan ma kenan…
Abubakar Shekau, Shugaban wani
bangaren Kungiyar Boko Haram ya fito a wani sabon kaset inda yayi jawabi cewa
shi ya kashe Babban Jami’in Sojin Najeriyar nan watau Laftana Kanar Muhammad
Abu Ali. An kashe gwarzon ne a Ranar 4 ga wannan watan na Nuwamba a Garin Malam
Fatori da ke Borno.
A wani jawabi da ya samu
kaiwa ga Jaridar Sahara Reporters, Shekau yace sune suka aika da Babban Sojin
lahira, duk da bai fadi ainihin sunan jarumin ba. Abubakar Shekau din yace
Bangaren sa na Kungiyar Boko Haram din ne ke kai duk wasu hare-hare da ake ji
kwanan nan ga Sojojin Najeriyar.
Abubakar Shekau yace yanzu
ma aka fara, wasu hare-haren na nan tafe. Shugaban wani bangaren Kungiyar na Boko
Haram yayi kaca-kaca da Sarkin Kasar Saudiya bayan ya taya Sabon Shugaban Kasar
Amurka mai jiran-gado murna.
Abubakar Shekau yace za su
koma kan Donald Trump har sai sun ga bayan sa, da zarar sun gama da Shugaban
Kasa mai ci na yanzu watau Barrack Obama. An dais ha cewa an kashe Shugaban na
Boko Haram, Abubakar Shekau. A kwanakin baya Kungiyar ISIL ta nada wani a
madadin sa a matsayin Shugaban Kungiyar Boko Haram din
Laftana
Kanar Abu Ali ya kasance jarumi wanda ya nuna bajinta wajen kawar da
Boko Haram daga Yankin Borno da Adamawa. Hakan ta sa aka kara masa
matsayi daga Manjo zuwa Laftanar Kanal din tun a shekarar da ta wuce. An
kashe sa tare da wasu Sojoji 6 a Farkon wannan Wata.
KU KARANTA LABARAI A SHAFIN MU NA NAIJ HAUSA
No comments:
Post a Comment