Tuesday, November 8, 2016

Yadda IBB ya daure ni a shekarar 1985-Buhari

Yadda aka tsare ni a Garin Benin-Inji Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya bada labarin abin da suka faru shekaru 30 baya

Shugaba Buhari ya bada labarin abin da ya faru a shekarar 1985 bayan an hanbarar da Gwamnatin sa

An tsare Muhammadu Buhari na watanni da dama a Birnin Benin bayan an yi masa juyin mulki

Marubucin tarihin Shugaba Buhari ya bayyana yadda abin ya faru



Shugaba Buhari ya je Garin Benin na Jihar Edo wani ziyara na kwana biyu domin kaddamar da ayyukan Gwamna mai barin gado-Adams Oshiomole. Shugaba Buhari ya bayyana yadda aka tsare sa a Garin Benin shekaru fiye da talatin da suka wuce bayan an kifar da Gwamnatin sa. 

Bayan kaddamar da ayyukan Gwamna Oshiomole, Shugaba Buhari ya tunawa Jama’a cewa ya zauna a wannan gari na Benin na wata da watanni. Buhari yace: Nayi matukar farin cikin zuwa bude wadannan ayyuka na Gwamna Oshiomole. Mutane da dama ba su san na zauna a wannan Gari ba har na watanni 40 a wani dan karamin gida, bayan an yi mani juyin mulki a shekarar 1985.

Mawallafin Littafin Tarihin Shugaba Buhari, Farfesa Paden a cikin Babin da yayi magana game da Kalubalen Shugabanci a shafi na 33 na Littafin da ya rubuta game da rayuwar Shugaba Buhari, yayi bayanin yadda aka tsare Shugaba Buhari a Garin na Benin bayan an hanbarar da Gwamnatin sa shekaru 31 da suka wuce. 

A lokacin nan, an tsare Muhammadu Buhari ne a wani dan gida, aka hada shi da wani dan karamin Talabijin domin sauraron labarai, sannan ana kawo masa jaridu, da abinci a kan kari. Buhari ya rika karanta Al-Qurani da littatafai a kodayaushe. Sai dai ba a bar Shugaba Buhari ya rika karbar ziyara ba, sai bakin da Shugaban Kasa Janar Babangida watau IBB ya amice. 

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ne ya kifar da Gwamnatin Janar Muhammadu Buhari a Agustan 1985, bayan Janar Buhari yayi watanni 20 a mulki. Muhammadu Buhari Yana tsare a Benin Mahaifiyar sa ta rasu.


No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...