Wednesday, November 23, 2016

Kungiyar ASUU ta janye yajin aiki



Ku koma aji, an gama yaji-Shugaban Kungiyar ASUU

– Da alamu akwai labari mai dadi daga Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’o’i

 

Shugaban Kungiyar ta ASUU yace an gama yajin aiki

 

– Kungiyar ASUU ta shiga wani yajin aiki na mako daya domin tattaunawa da Gwamnatin Tarayya

 

Farfesa Biodun Ogunyemi wanda shine Shugaban Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’a na Kasa ya bayyanawa manema labarai cewa an kare yajin aikin da Kungiyar ta shiga wancan makon. Shugaban Kungiyar ASUU din yayi wannan jawabi ne a Jiya, Talata 22 ga wata.

Kungiyar ASUU ta shiga yaji ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta gaza cika yarjejeniyar da suka yi da ita a shekarar 2009. Don haka ne Kungiyar ta Malaman Kasa suka shiga yajin aiki na mako daya. Yanzu dai mako daya ya cika, don haka Malaman Jami’an sun koma makaranta Inji Biodun Ogunyemi.

Shugaban Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’ar Kasar, Farfesa Ogunyemi yace abubuwa suna tafiya yadda suka dace, musamman yadda Majalisar Dattawa ta shiga cikin maganar. Ogunyemi yace nan da zama daya ko biyu za a gama tattaunawa, hakan zai sa mu fasa yajin gaba daya. 

Shugaban Kungiyar dai yace ya ji wasu suna cewa ASUU ta cigaba da yaji bayan mako guda, to ba haka ne gaskiyar magana ba. Sai dai Shugaban Kungiyar ASUU na Bangaren Jami’ar  Nsukka, Dr. Ifeayi Abada, yace su fa sun cigaba da yajin, har sai baba ta gani za su dawo.

[NAIJ Hausa]

2 comments:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...