Tuesday, November 15, 2016

Za a fuskanci matsanaciyar yunwa shekarar 2017


Fadar Shugaban Kasa tace ‘Yan Najeriya su shiryawa matsanaciyar yunwa

Idan ba a dauki mataki ba, ‘Yan Najeriya za su shiga wani mummunan hali na matsanaciyar yunwa badi


Mai magana da bakin Shugaban Kasar, Garba Shehu yayi wannan bayani a wani Gidan Rediyo


Kasar Najeriya ta fi kowa noman hatsi a kaf fadin Afrika, sai dai…

 

Mai magana da yawun-bakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya bayyanawa ‘Yan Najeriya cewa da yiwuwar Kasar ta fuskaci matsanaciyar yunwa zuwa farkon shekara mai zuwa. Mai ba Shugaban Kasar shawara a game da harkar yada labarai yayi wannan bayani ne a jiya a Gidan Rediyon Freedom da ke Kano.

Mai ba Shugaban Kasa Buhari shawara a game da harkar yada labarai yace ana da bukatar hatsi a kasuwannin duniya, wanda kuma zai kara kamari. Hakan ta sa wasu ‘Yan Najeriya ke fitar da abinci zuwa Kasashen waje. Garba Shehu yace idan ba a dauki mataki ba, Najeriya za ta rasa abin da za ta ci shekara mai zuwa. 

Kasar Najeriya ta fi kowace Kasa a fadin Nahiyar Afrika noman hatsi, an kuma yi dace an samu damina mai albarka. Sai dai kuma saboda yanayin yadda ake neman hatsin a wasu wurare, ‘Yan Kasar suna fitar da abinci zuwa ketare, hakan na iya janyo matsanaciyar yunwa a Kasar.

Ministan noma, Audu Ogbeh ya koka da wannan lamari. Yanzu haka Kasashen Afrika irin su Libya da Algeria, kai har irin su Kasar Brazil suna neman shinkafa daga Najeriya. Hakan ta sa wasu 'Yan Kasar ke fita da hatsi wajen Kasar ta kan iyaka. Kasuwanni da ke Kasar Kano da Sokoto kullum a kan fita da tirela ba adadi na kayan hatsi da aka noma a Kasar.

Mai magana da yawun-bakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu yace ana iya fama da matsanaciyar yunwa badi, idan ba a dauki mataki ba. Yanzu dai an haramta shigowa da shinkafa ta kan iyakar Kasar.

A duba shafin NAIJ Hausa domin samun labarai



1 comment:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...