Ko
shin wanene sabon sirikin Buhari?
– Diyar Shugaba Muhammadu Buhari, Zahra za ta auri dan Gidan hamshakin Attajirin nan, Muhammad Indimi
– Muhammadu Indimi kasurgumin Attajiri ne a Kasar Borno
– Ahmed Indimi yana daga cikin ‘Ya ‘yan wannan mai kudi
Ana
ta samun rahoto cewa Diyar Shugaban Kasa, Zahra Buhari za tayi aure nan da
kwanaki kadan masu zuwa. Zahra Buhari dai tayi fice ko a cikin ‘ya ‘yan
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Mun kawo maku bayani, ko shin wanene wannan
sabon sirikin na Buhari?
Ahmed
Indimi yayi karatun share fagen Digiri a Legas, a wata Makaranta ‘Global International’, daga nan ya wuce
Jami’ar InterContinental ta Amurka da ke Atlanta domin yin digiri na farko a
Bangaren Fasahar Komfuta da bayanai.
Ahmed
Muhammad Indimi shine Shugaban Kamfanin ‘Oriental
Energy Resources’ masu harkar Man fetur. Ahmed Indimi dai saurayi ne
kyakkyawa kuma son kowa. Sannan Ahmed yana da ban dariya da kuma son dariya.
Ahmed
Indimi mutum ne mai son karatun tsiya, bayan yayi digiri, ya koma yayi digiri
na biyu kan harkar kasuwanci da ake kira MBA game da Harkar tsaron yanar gizo a
Jami’ar nan dai ta Amurka. A wannan Makaranta ya rike matsayin Ma’aji na
Kungiyar dalibai, Tun shekaru uku da suka wuce kuwa, Angon Zahra ya ba Miliyan
dari baya. Kyaun da ya gaji uban sa, Ahmed Muhammad Indimi. Ko ba a fada maka ba, daga jin sunan Indimi, ka san kuwa akwai 'dimi'
[Karanta NAIJ Hausa domin samun kayatattun labarai]
No comments:
Post a Comment