Monday, November 14, 2016

An karrama shaharren dan wasan Kwaikwayo


Shahararren dan wasan Kwaikwayo Jackie Chan ya karbi kyautar Oscar

 

Shahararren dan wasan Kwaikwayo na Kasar China, Jackie Chan ya karbi lambar yabo


An karrama Dan wasa Jackie Chan da sauran wasu ‘Yan wasan kwaikwayo a karshen wannan makon


– An ba Jackie Chan lambar girma ne a Garin Hollywood na Amurka

 

A Ranar Asabar dinnan da ta wuce aka karrama shahararren dan wasan kwaikwayo Jackie Chan na Kasar China. An ba shararren dan wasan lambar yabo ne na Oscar saboda jaruntar sa a fagen wasa a Birnin Hollywood na Kasar Amurka. 

Daga cikin wadanda aka ba lambar yabon akwai wani Editan Fina-finai, Anne V. Coates, da kuma wani Darekta, Lynn Stalmaster da wani kwararren mai hada fim na Amurka, Fredrick Wiseman. Sai shi dan wasa Jackie Chan kan sa. Jaridar XINHUA net ta Kasar China ta dauko wannan labari.

An ba wadannan gwanaye lambar girma ne saboda irin rawar ta suka taka a fagen wasan kwaikwayo. Wannan ne karo na takwas da aka yi irin wannan taro na lambar girma na Gwamnoni da ake yi a Hollywood watau 'Oscar'. Masu hada abin suka ce ba za a manta da irin su Jackie Chan ba. 

Jackie Chan kwararren dan wasa ne, marubuci, mai hada fim, kuma Darekta. Tun yana dan shekara 8 yake wasan kwaikwayo a Hong-Kong, kafin ya fita duniya gaba daya.  Jackie Chan ya fi shekara 56 yana wasan fim, ya kuma fito a fina-finai sama da 200.

Jackie Chan yace ba zai taba manta wannan rana ba, bayan ya karbi kyautar sa. Yace abin kamar a mafarki.Dan wasa Jackie Chan ya godewa mutanen Garin su na Hong-Kong, da ma Kasar su ta China da kuma sauran mutane. A yayin yin wadannan fina-finai J. Chan ya sha samun karaya ba sau daya, ba biyu ba.


A leka shafin NAIJ Hausa domin samun labaran Hausa

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...