Tsuntsayen soyayya
– Ola Moses zai auri Temi bayan sun kwashe shekara-da-shekaru suna soyayya
– Shekarar tsunstayen goma suna soyewar su
Kamar
dai yadda Hausawa kan ce: Abu karamar
wasa, karamar magana ta zama babba…Wadanna bayin Allah sun shafe shekaru
fiye da goma suna tare, ga shi Allah yayi za su kuma yi aure.
Kamar
yadda Sahibar ta fada, Temi tace tun shekarar 2006 suka hadu a Coci wajen
bauta, Moses ya kuwa tambaye ta lambar waya, nan take ta mika masa. A wancan
lokaci ana yayin waya kyauta da tsakar dare… Shekaru goma kenan, ga shi yau, za
suyi aure.
Timi
tace kafin sa, ba ta taba soyayya a duniya ba, kuma shine na karshe. Timi tace
Moses ya nuna mata yadda ake soyayya a rayuwa, kuma da shi kadai ta taba yi.
Timi tace lokacin da Ola Moses ya tafi Kano, ta zaci ba zai dawo ba.
Suka
ce an ta kokarin a ga bayan su a rayuwa, sai dai Ubangiji ya kaddara za su auri
juna. Tace har jina-jina iyayen ta sun taba yi mata, amma ya zama Tarihi.
Kai kadai na rike a raina, kaunar ka nike yabawa... Allah ya hada Temi da Moses.
No comments:
Post a Comment