Thursday, November 3, 2016

Jihar Neja za ta noma ton miliyan guda na shinkafa




Noman Rani: Jihar Neja za ta noma shinkafar da za ta ci

 

Manoman Jihar Neja za su noma ton miliyan daya na shinkafa  wannan shekarar

 



– Gwamnatin Jihar Neja na kokarin ganin Jihar ta noma abin da za ta ci

 



– Gwamnatin Jihar za ta samar da aiki ga matasa da hanyar noman rani

Gwamnatin Jihar Neja na shirin noma ton miliyan daya na shinkafa wannan shekarar, Gwamnatin Jihar na kokarin ganin Jihar Neja ta noma duk shinkafar da za ta ci a shekarar da kan ta. Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya tabbatar da hakan a wannan makon. 

Gwamnatin Jihar Neja za ta noma shinkafar ne a cikin ranin nan, ana sa ran Gwamnati za ta samar da kayan aikin gona kamar yadda Ministan gona, Audu Ogbeh ya bayyana. Gwamnati za ta samar da kayan noman rani, irin su; Injin ban ruwa, da na cashe shinkafa, wannan zai taimaka wajen noma a wannan shekara. 


Hakan zai sa farashin kayan abincin su sauka Kasa inji Gwamnatin. Babban Bankin Kasar watau CBN ta tallafawa matasa da kudin noma a Jihar wannan shekarar a Karamar Hukumar Lavun na Jihar Neja. Bankin CBN din ta kashe fiye da Biliyan biyu wajen noman shinkafa a fadin Kasar nan. 

Yanzu haka mutane, musamman matasa sun samu abin yi a Jihar Neja ta noma; kusan mutane 2000 sun amfana ta noman shinkafa, yayin da fiye da 900 suka yi noman auduga. Akwai dai fili sama da kilomita 90,000 na noma a fadin Jihar.


A karanta labaran Hausa a shafin NAIJ Hausa

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...