Wednesday, November 2, 2016

A sauka lafiya, duk wanda zai bar Najeriya-Shugaba Buhari


Muna nan, sai mun gyara Kasar nan-Shugaba Buhari



Shugaba Buhari yace duk mai shirin barin Najeriya, ya sauka lafiya

 

Shugaba Buhari yace amma fa su suna nan, babu inda za su je, sai Najeriya tayi kyau

 

Shugaban Kasa ya fadi hakane lokacin da ya gana da Shugabannin Neja-Delta


Shugaba Buhari yace duk wanda yake ganin yana da wurin zuwa da ba Najeriya ba, to sai yayi tafiyar sa, ya sauka lafiya, amma fa su suna nan har sai sun gyara Najeriya. Mai magana da bakin Shugaban Kasar, Mallam Garba Shehu ya bayyana wannan jawabi na Shugaban Kasar.

Shugaba Buhari yayi wannan magana ne a lokacin da ya gana da Shugabannin Yankin Neja-Delta a jiya. An yi wannan tattaunawa domin ganin an samu wanzuwar zaman lafiya a Yankin na Neja-Delta. Shugaba Buhari yake cewa duk wanda yake da wata Kasa da ba Najeriya ba, sai ya fice, ya tafi can.


Shugaba Buhari kuwa yake cewa za su tsaya a Kasar har sai sun gyara ta, Shugaban Kasar ya koka da irin halin da ake ciki; yake cewa har ta kai Jihohi da dama ba su iya biyan albashin ma’aikatan su.


A Karanta cikakkun labarai a NAIJ Hausa

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...