Fadar
Shugaban Kasa tace ‘Yan Najeriya su shiryawa matsanaciyar yunwa
– Idan ba a dauki mataki ba, ‘Yan Najeriya za su shiga wani mummunan hali na matsanaciyar yunwa badi
– Mai magana da bakin Shugaban Kasar, Garba Shehu yayi wannan bayani a wani Gidan Rediyo
– Kasar Najeriya ta fi kowa noman hatsi a kaf fadin Afrika, sai dai…
Mai magana da yawun-bakin
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya bayyanawa ‘Yan Najeriya
cewa da yiwuwar Kasar ta fuskaci matsanaciyar yunwa zuwa farkon shekara mai
zuwa. Mai ba Shugaban Kasar shawara a game da harkar yada labarai yayi wannan
bayani ne a jiya a Gidan Rediyon Freedom da
ke Kano.
Mai ba Shugaban Kasa Buhari
shawara a game da harkar yada labarai yace ana da bukatar hatsi a kasuwannin
duniya, wanda kuma zai kara kamari. Hakan ta sa wasu ‘Yan Najeriya ke fitar da
abinci zuwa Kasashen waje. Garba Shehu yace idan ba a dauki mataki ba, Najeriya
za ta rasa abin da za ta ci shekara mai zuwa.
Kasar Najeriya ta fi kowace
Kasa a fadin Nahiyar Afrika noman hatsi, an kuma yi dace an samu damina mai
albarka. Sai dai kuma saboda yanayin yadda ake neman hatsin a wasu wurare, ‘Yan
Kasar suna fitar da abinci zuwa ketare, hakan na iya janyo matsanaciyar yunwa a
Kasar.
Ministan noma, Audu Ogbeh ya
koka da wannan lamari. Yanzu haka Kasashen Afrika irin su Libya da Algeria, kai har irin su Kasar Brazil suna neman
shinkafa daga Najeriya. Hakan ta sa wasu 'Yan Kasar ke fita da hatsi wajen Kasar ta kan iyaka. Kasuwanni da ke Kasar Kano da Sokoto kullum a kan fita da tirela ba adadi na kayan hatsi da aka noma a Kasar.
Mai magana da yawun-bakin
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu yace ana iya fama da matsanaciyar yunwa
badi, idan ba a dauki mataki ba. Yanzu dai an haramta shigowa da shinkafa ta kan iyakar Kasar.
A duba shafin NAIJ Hausa domin samun labarai
Allah ya kyauta toh
ReplyDelete