Harin
Bam ya kashe wani Gwamna a Kasar Turkiyya
– ‘Yan ta’adda sun tada bam a Ofishin wani Gwamna a Kasar Turkiyya
– ‘Yan Sanda sun kama mutane da dama da ake zargi da wannan laifi
– Wannan abu ya faru ne a Kudancin Kasar Turkiyya
Harin bam yayi sanadiyar
mutuwar wani Gwamna a Kasar Turkiyya. Wannan mummunan abu ya faru ne a kwanan
nan. Tuni dai Jami’an ‘Yan Sanda suka kama wadanda ake zargi har mutane 30.
‘Yan ta’addan sun tada bam din ne a Ofishin Gwamnan, hakan yayi sandaiyar
mutuwar sa da wasu mutanen.
Kungiyar Matasa ta YPS ta
Jam’iyyar Kabilar Kurdawa watau PKK sun dauki nauyin wannan aika-aika. An dai
kai wannan hari ne a Ranar Alhamis da ta wuce a Garin Mardin da ke Kudancin
Kasar na Turkiyya. Jaridar ANF mai kusa da ‘Yan ta’addan suka rahoto hakan.
A harin dai an rasa Gwamna
Muhammad Fatih Safiturk na Yankin Derik. Ya samu mugayen rauni na kuna da bam
din ya tashi, nan aka garzaya da shi asibitin da ke Birnin Gazientep ta
helikwafta. Amma dai bai tashi ba, Jiya ya samu cikawa Inji Jaridar Dogan.
A Afrika kuwa, Rahotanni na
nuna cewa Mayakan Boko Haram sun mika kawunan su da iyalan su, sun kuma ajiye
makaman Yaki a Yankin Chad. ‘Yan Boko Haram din fiye da
240
suka ce wa Rundunar hadin gwiwa cewa ba su iyawa. A baya dai Boko Haram ta
kashe mutane kimanin fadin Kasar Belgium ta Turai.
Allah ya kyauta
ReplyDelete