Monday, November 21, 2016

Shugabanci: Na tafi kenan Inji Jonathan

Kuma daina tunani zan dawo Inji Jonathan




PDP ta tuna da Shugaba Jonathan, inda tace anyi Gwarzo


Jiya Goodluck Jonathan ya cika shekaru 59 a duniya


Jam’iyyar PDP tace Shugaba Buhari ba zai samu nasara wajen Yaki da cin hanci da rashawa a Kasar nan ba

 

Jam’iyyar PDP ta tuna da Tsohon Shugaba Jonathan Goodluck yayin da ya cika shekaru 59 a jiya. Shugaban Bangaren Jam’iyyar PDP din, Sanata Ahmad Makarfi yace Shugaba Jonathan din ba karamin jan gwarzo bane.

PDP tace har yanzu ana shan romon ayyukan da Shugaba Jonathan yayi wajen fannin tsarin mulki da siyasa, ilmi, da kuma sauran hanyoyin more rayuwa. PDP tace Shugaba Jonathan yana cikin wadanda suka mika mulki salin-alin a Nahiyar Afrika, ko don haka tauraruwar sa ta ke kara haske a duniya.

Ana ta rade-radin cewa Goodluck Jonathan din zai dawo, sai dai a shafin sa na kafar Facebook ya rubuta cewa shi fa ya tafi kenan, sai labari. Shugaba Jonathan yace ai yanzu mulki kuma sai ‘ya ‘yan su da jikoki, don su kam sun yi sun gama. Jonathan yace Kasa ai ba ta cigaba da Tsofaffi a mulki.

Haka kuma, Jam’iyyar PDP mai adawa a Kasar tace babu inda Shugaba Buhari zai kai wajen Yaki da cin hanci da rashawa a Kasar nan domin ya saka son kai a lamarin.

[NAIJ Hausa]

1 comment:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...