Tuesday, November 8, 2016

Shugaba Buhari ya koma karo karatu?


Sai ga Shugaba Buhari a cikin ajin dalibai

Shugaba Buhari ya kai ziyara Jihar Edo inda ya kaddamar da ayyukan Gwamna Adams Oshiomole

Oba na Benin yace Shugaba Buhari na kokari wajen fada da cin hanci a Kasar nan



Sai ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cikin aji tare da daliban Sakandare, shin ko ya je rubuta takardar da ‘Yan adawa suka ce ba shi da ita ne na shaidar WASSCE watau ta kammala Sakandare? Abin mamaki kuma an ga Shugaba Buhari yana rubutu cikin wani littafi, ko dai jinga ne Malam ya bada?

A cikin ajin dai Shugaba Buhari ya zauna tare da Gwamnan Jihar kan sa, Adams Oshiomole daga gefen sa. Daliban dai sun kasance suna ta kurawa Shugaban Kasar Najeriya ido yayin da ya zauna cikin su. Ko yana rubuta sunayen masu surutu ne a ajin, ko kuwa yana bincika wadanda ba su halarci darasi ba ne?


Shugaba Buhari ya kai ziyarar kwana biyu Jihar Edo inda ya kaddamar da ayyukan Gwamna Adams Oshiomole mai shirin barin gado, ciki har da Makarantar New Era Secondary School da aka maida Samuel Ogbemudia Secondary School.

Shugaba Buhari ya kuma kai ziyara wajen sabon Sarki, inda ya taya Sarkin murna, wanda shine Oba ne Benin na 40 a Jerin sarautar.  Shugaba Buhari ya tunawa Jama’a cewa ya zauna a wannan gari na Benin na wata da watanni bayan an masa juyin mulki. Oba na Benin din ya godewa Shugaba Buhari.



 Gwamna Oshiomole na kokarin satar amsar Baba Buhari :P


1 comment:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...