– Kasar Switzerland ta karbe motocin Mataimakin Shugaban Kasar Equatorial Guinea
– Jami’an Kasar sun karbe motocin Mataimakin Shugaban Kasar na Afrika har guda 11
– Mataimakin Shugaban Kasar dai dan Shugaban Kasar na Equatorial Guinea ne
Cin hanci da rashawa dai ya
yabaibaye mutanen Afrika bisa dukkan alamu, ba kuma ‘Yan Kasar Najeriya ne
kadai ba su son sauka daga Mulki ba da zaran sun dare, igiya ta ja su. Har wasu
Kasashen na Afrika sun ganewa daura ‘Ya ‘yan su da Iyalan su kan kujerar mulki
in har dai suna raye.
Wani abu sai Afrika; 'da da uba: Shugaban Kasa da Mataimakin sa
Yanzu haka, Kasar
Switzerland ta karbe motocin Mataimakin Shugaban Kasar Equatorial Guinea,
Teodorin Obiang Nguema. Mataimakin Shugaban Kasar Mista Teodorin dan Shugaba
Obiang Nguema ne na Kasar na cikin sa. Yana da shekara 47 a duniya, Mahaifin sa, wanda shine Shugaban
Kasar ya nada sa a matsayin mataimakin sa.
Teodorin Obiang Nguema ya
zama Mataimakin uban sa ne a shekarar 2012, tun nan kuma
ya shiga facaka da Dalolin kudi. Yanzu haka yana soyayya da wata mawakiya 'Yar Kasar Amurka. Kwanan na Jami’an Kasar Switzerland ta samu
karbe wasu daga cikin motocin Mista Teodorin har guda 11.
Teodorin Obiang Nguema da Ba'Amurkiyar Budurwar sa, Eve
Ciki motocin da aka karbe, har da motar
dala miliyan $2.8, wanda ake ce duk duniya guda 7 kadai aka taba kerawa. Akwai irin
su Buggati Veyron da Ferrari masu dan banzan tsada.
Duk Afrika dai babu Shugaban
da ya kai Obiang Nguema dadewa a kan mulki, ya hau mulkin Kasar ne a shekarar
1979. Kasar mai arzikin man fetur da mutane Miliyan daya da ‘yan kai ne rak na
fama da masifan talauci.
A karanta labaran Hausa a shafi na na NAIJ Hausa
M. Malumfashi
M. Malumfashi
Gaskiya shuwagabannin arewa, cin hanci da almubazaaranci da kudin mutane yayi shiga cikin jikin su.. Allah ya kawo mana karshen wannan abu.. Ameen
ReplyDelete