Saturday, November 12, 2016

ASALIN ASARA-Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N

Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N Zangon-Shanu, Zaria

 

Daga Bakin Sheikh S.S Abubakar








Bayan shaidawa da gaskiya cewa lallai babu abin bauta da gaskiya face Allah mai girma, shi kadai yake ba sa da abokin Tarayya. Mulki duk gare sa yake, Godiya da yabo sun tabbata a gare sa, shine mai iko kan komai. Muna shaidawa cewa lallai Shugaban mu Annabi Muhammadu SAW Bawan Allah ne kuma Manzon sa. Shi ne mai albashir ga bayin da kuma gargadi ga ta’alikai. 

Bayan haka:
Mu ji tsoron Allah SWT, mu kuma rabe duk wasu burace-buracen mu na rayuwa gare sa, Mu kuma ji tsoron azabar Sa.
Allah SWT yace:
Ku nemi arziki daga Allah SWT, ku bauta Ma sa, kuma ku gode Ma sa, gare sa ne kuma makoma take.

‘Yan uwa Huduba tana jan hankali ne game da rayuwa. Rayuwa ta duniya tana kai komo ne tsakanin riba da asara. Duk mai hankali ya kan ga ya dage ya nisantar da kan sa ga duk wata asara, ya kuma tabbata ya rabauta a duniya. Mutum ya kan yi farin ciki a game da ribar da ya samu tare da walwala, sannan kuma yayi bakin ciki yayin da ya gamu da asara. To, sai dai abin fahimta shine asarar hakika ba asarar wani abu na duniya bane; na matsayi, mukami, dukiya, kasuwanci, ko aiki. Asara ta hakika, itace asarar abin da yake wanzanje nan gaba na lahira. Duk wani dan jin dadi na nan duniya, ba ma’auni ba ne na gane riba ko asara a rayuwa. Akwai wadanda ke gani sun samu riba ta duniya, amma a hakika, sun yi asarar rayuwar su ta lahira, wancan kuma it ace rayuwa ta har abada. 

Allah SWT yana cewa, lallai ka fada masu ya Manzon Allah SAW:
Masu asara lallai sune wadanda suka yi asarar kan su da iyalin su Ranar tashin kiyama. Allah Madaukaki yace; A saurara, wannan shine asara mabayyani!

Ko ta ya mutum yake asarar kan sa da Iyalan sa?
Ya zama mutum ya kare rayuwar sa ba bisa tafarkin Allah SWT da Manzon Tsira SAW ba.
Saboda haka riba da asara a ma’aunin masu hankali shine mutum ya ci ribar imani. Wanda bai san da wannan ba kuwa, shi yayi asarar rayuwar sa da makomar sa, ko me kuwa ya tara ya jibge na arzikin rayuwar duniya.

Allah SWT yana cewa a cikin Suratul Asr:
…Lallai, Dan Adam yana cikin asara, face wanda yayi imani, ya aikata aiki na-gari, sannan suka rika yi wa juna wasici da hakuri da juriya wajen tsayawa a tafarkin Allah SWT, suka kuma gaskatar da imani suka lazumci tafarkin tsira, sune masu babban rabo. 

Mafi girman asara shine asarar addini, ya zama mutum bai tunanin addini a duk abin da zai aikata. Ana so ko menene mutum zai yi, ya auna wannan aiki da sha’war Allah SWT da Manzon sa SAW.
Annabi Muhammadu SAW ya kan ce:
Allah ka da ka sa musibar mu ta zama a cikin addinin mu.

Haka duk wanda yayi watsi da aiki na kwarai, zai yi nadama a Ranar da za a bijirar da ayyukan mutane bayi. A wannan rana duk wanda ayyukan sa na zunubi suka kerewa na alkhairi, yana cikin masu asara. 

Allah mai iko SWT yace:
Duk wanda ma’aunin sa na alheri, suka yi nauyi, sune masu babban rabo, amma duk wanda ayyukan sa na banza suka fi nauyi, wannan yana daga cikin masu asara saboda zaluncin da yayi.

Ya ake zalunci ga ayar Allah?
Zuciyar mutum ko shaidan ya fadawa mutum abin da zai yi lokacin da Allah SWT ya bada umarnin wani abu sabanin haka, wannan shine ainihin zalunci. Wajibi ne ayi imani da umarnin Allah a kuma sabawa duk wani umarni na dabam, wanda yayi akasin haka, yayi zalunci. Daga cikin alamun masu asara, akwai saba alkawari. Ko kuma mutum ya zama mai warware yarjejniyar da ya dauka a da, ko mutum ya zama mai lalata abin da aka kulla, ko kuma mutum ya zama mai yada barna a cikin Kasa. 

Ya kuma kamata a kiyaye abu na gaba:
Biyayya ga kafirai, wanda Allah SWT yake cewa:
Idan ku ka yi biyayya ga wadanda suka kafirta, za su maishe ku ga diga-digan ku, sai ku zama cikin masu asara.
Akwai wadanda duk ayyukan su na rayuwa, suna duba maslaha ne da za a samu na duniya, watau duk abin da ba za a samu wani alheri na duniya ba, komai yawan ladan sa, sai su hakura. Idan kuma aka ce maka akwai wani samu na duniya, sai su aikata wannan aiki ko da ban don neman yardar Allah ba ko wani lada.

Allah yake cewa a cikin Qur’ani:
Daga cikin mutane, akwai wadanda akwai masu bautawa Allah ta ra-ra-gefe. Idan suka samu alheri, sai su ji dadi, idan kuma jarrabawa ta afka masu, sai su juya fuska. Wannan shine ainihin asara ta duniya da lahira. 

Hakanan kuma duk wanda dukiyar sa ko ‘ya ‘yan sa suka shagaltar da shi, ya tozarta abubuwa na biyayya ga Allah.
Allah SWT yace: Ka da dukiyoyin ku da iyalan ku su hana ku tuna Ubangiji Allah SWT.
Duk wanda ya jibanci shaidan a maimakon Allah Madaukaki, wannan yayi asara mabayyaniya.
Haka kuma duk Al’ummur da ta kangarewa Allah Mai Girma, karshen ta nadama. 

To ina mafita?
Mu ji Tsoron Allah SWT wajen gudanar da komai na rayuwar mu yadda Allah ya bada umarni. Wannan shi ya kamata da rayuwar mu a ko yaushe. Hakan ne kadai zai kawo mana natsuwa daga firgici da rashin kwanciyar hankali. Wannan kuwa itace Sunnar Allah.


Allah ya bamu ikon AlKurani mai Girma da aiki da shi. Allah ya dada tsira ga Annabi Muhammad SAW da iyalan sa da Halifofin sa, da sauran wadanda suka bi su da kyautatawa. Allah ka taimaki Musulunci da Musulmai.
-Sheikh Salihu S. Abubakar

Masallacin Islamic Trust of Nigeria, ITN, Zaria.

Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba



7 comments:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...