Friday, November 18, 2016

An rusa Makarantar Shi’a a Garin Zaria


‘Yan Zaria sai murna suke yi an dagargaza makarantar Fudiyya ta Shi’a


– Mabiya Kungyar IMN ta shi’a sun saba fito-na-fito da Hukuma a Kasar nan


– Don haka Gwamnati ta haramta ayyukan ‘Yan shi’a a Jihar Kaduna


– Ana tunanin Kungiyar na da goyon baya daga Kasashen ketare

 

Jama’a sun shiga tsalle suna murna a Garin Zaria bayan da aka rusa wata Makaranta ta Kungiyar IMN ta ‘Yan shi’a. Hukuma dai ta rusa Makarantun na Firamare da Sakandare na shi’a ne a Jiya, Alhamis. 

An rusa wannan Makaranta mai suna Fudiyya da ke Babban Dodo da ke Gangaren Fadama cikin Zaria City. Gwamnatin Jihar ce dai ta bada umarni rusa wannan cibiyar Makaranta. Wannan makaranta Fudiyya ta mabiya shi’a ce.


A kwanakin baya Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya haramta ayyukan shi’a a fadin Jihar. Gwamnoni da dama kuma suka yi ta bin sahu a fadin Arewacin Kasar. ‘Yan unguwar dai sun yi tsalle da farin ciki da aka ruguza wannan makaranta. An dai ruguza wannan makaranta da tsakar rana.

Wani mazaunin wurin mai suna Musa Musa, yace: madalla, abu yayi daidai, dama sun dade suna jiran wannan rana. Wani mutumi kuma da ake kira Baba Bala yace Gwamnati tayi daidai, ka da kuma ta fasa.


Shugaban Kungiyar dai ta Islamic Movement of Nigeria (IMN) yana nan a tsare tun shekar bara. Kwanan an kara samun wata takkadama tsakanin ‘Yan Shi’a da ‘Yan Sanda a Garin Kano inda da dama suka rasu. Gwamna Fayose na Jihar Ekiti dai yace ya kamata Kotun Duniya ta duba irin kisar gillar da ake yi wa 'Yan Shi'a a Najeriya

[Karanta NAIJ Hausa domin samun labarai a kai-a kai]

3 comments:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...