Mourinho ya shiga uku
– Hukumar FA ta sake cin Kocin Man Utd tara saboda kalaman sa
– FA tace kalaman Jose Mourinh ga Alkalin wasa Taylor sun yi muni
– Ba wannan ne karo na farko da aka ci Kocin tara ba
Hukumar
FA ta Ingila ta sake kuma cin tarar Kocin Kungiyar Manchester United, Jose
Mourinho. Hukumar da ke kula da kwallon kafa na Ingila tace kalaman Kocin, Jose
Mourinho ga Alkalin ta ba su yi mata kyau ba ko kadan.
Jose
Mourinho ya fadi wasu kalamai ne ga Alkalin wasa Anthony Tailor. Hukumar FA
tace duk yadda Alkalan suka yi ba za su burge Kocin ba. Anthony Tailor ne ya
busa wasan Kungiyar Man Utd da Liverpool inda aka tashi babu ci a Gidan
Liverpool.
Kocin
na Man utd zai biya tarar pound fam 50,000, wanda wannan ba kananan kudi ba ne.
Jose Mourinho ya zargi Alkalin da addabar ‘Yan wasan san a Man Utd. BBC ta
rahoto a Jiya cewa bayan tarar, an gargadi Kocin da ya bi a sannu.
Ba
dai wannan ne karo na farko da Kocin ya saba shiga cikin irin wannan matsalar
ba. Ko shin zai gyara?
Karanta NAIJ Hausa domin samun labarai da harshen Hausa
hahaha, this pic very funny
ReplyDelete