– Tsohon Shugaban Cuba Fidel Castro ya bar duniya Ranar Jumu’a
– Fidel Castro ya rasu yana da shekaru 90
– Tsohon Shugaban ne ya jagoranci juyin juya-halin da aka yi a Kasar Cuba shekaru 50 da suka wuce
Shin Wanene Fidel Castro?
Castro kenan yana busa karar sa 'yar gida
Yayin da ake zaman makokin
Fidel Castro a Kasar Cuba. Mun kawo maku dan takaitaccen Tarihin sa.
- An haifi Fidel Castro a shekarar 1926, a Garin Oreiente da ke Yammacin Kasar Cuba
- An daure Fidel Castro a shekarar 1953 bayan yayi yunkurin kifar da Gwamnati
- A shekarar 1955 aka saki Fidel Castro daga Gidan Yari
- A shekarar 1959 ya samu kifar da Gwamnatin Shugaban Kasar lokacin, ya zama Shugaba
- A shekarar 1961 ya yaki harin da wata Kungiya da CIA ta Amurka ta marawa baya ta kawo masa
- A shekarar 1976 Majalisar Kasar Cuba ta zabi Fidel Castro a matsayin Shugaban Kasa
- A kuma shekarar 1976 ya kulla yarjejeniya da Kasar Amurka game da ‘Yan gudun Hijira
- A shekarar 2006 ya sauka daga Shugabancin Kasar Cuba
- Dan uwan sa Raul Castro ya gaje sa
- Fidel Castro ya mutu a shekarar 2016 yana mai shekaru 90 a duniya.
[BBC]