DUNIYA MOTA
Duniya shiga dakin mota; shiga da kai, fitowa da
baya…-Mawaki Alhaji Sani Sabulu
Wani mutum ne yashirya yin wata tafiya. Ya dauki
matarsa da ’ya’yansa cikin motarsa suka kama hanya. Ba su yi nisa ba suka hadu
da wani mutum tsaye a bakin hanya. Ya daga musu hannu suka tsaya, ya nemi su
dauke shi. Maigida ya tambaye shi: “Wane ne kai?” Ya ce, “Ni ne dukiya.” Nan
take iyalin suka dau shewar cewa ga abokin tafiya, maganin takaicin duniya. Suka
ce lallai a dauke shi su tafi tare. Dama motar irin babbar Jif din nan ce mai
yalwar mazaunai wato (family car), sai suka dauke shi suka tafi. Suna yin gaba
kadan sai suka tarar dawani mutumin, shi ma a bakin hanya yana dagamusu hannu,
sai maigida ya tsaya. Ya tambaye shi: “Wane ne kai?” Ya ce: “Ni ne sarauta da
matsayi.” Iyalan na jin haka suka ce a dauko shi. Domin babu abin da yin sa zai
gagarimutum a duniya, muddin yana da sarauta da matsayi. Shi ma suka dauke shi
suka wuce. Suna kara gaba kadan sai ga wani mutumin tsaye a gefen hanya, shi ma
ya daga musu hannu suka tsaya. Maigida ya tambaye shi: “Wane ne kai?” Ya ce: “Ni
ne Addini.” Maigida ya waiwayi iyalansa, sai ya ga sun yi jugun-jugun cike da
damuwa. Tun kafin ya nemi shawararsu suka ce: “Wannan ba abokin tafiya ba ne.
Takura mana zai yi da hukunce- hukuncensa na halal da haram,ya hana mu more
rayuwarmu. Ya dai jira nan gaba ma dawo mu dauke shi bayan mun gama more jin
dadin rayuwarmu.” Maigida ya yarda da shawarar iyalansa, suka wuce suka bar Addini
nan tsaye, suna taQama da wadatar dukiya da alfarmar sarauta da matsayi, har
suka ci karfin tafiyar daza su yi.
Suna cikin tafiya sai suka iso wani wurin binciken
ababen hawa (Cheking Point). Suka tsaya don suma a duba su. Sojan da ke bincike
yace da maigida: “Kai fito mu tafi, tafiyarka ta kare daga nan!” Maigida ya ce:
“Kai kuwa wane ne kai?” Yace: “Ni ne mala’ikan mutuwa.Ina bincike ne a kan
addini. Kai kuwa ba ka da shi.” Maigida ya ce: “Affff", ai na baro shi a
hanya. Bari na koma na dauko shi.” Mala’ikan mutuwa ya ce: “Ai wannan damar ta
wuce ka har abada!” Maigida ya kara cewa: “To ai ina tare da dukiya da sarauta
da matsayi da dukkan iyalina.” Mala’ikan ya ce: “Ai duk wadannan ba za su
amfane ka da komai ba. Addini kadai ake bukata a nan.” Maigida ya waiga sai ya
ga matarsa ta haye mazauninsa na direba, ta ja mota sun yi tafiyarsu ita da
sauran iyali tare da dukiya da sarauta da matsayin. Suka bar shi nan mala’ikan
mutuwa ya tasa keyarsa. Babu iyali! Babu dukiya!! Babu sarauta da matsayin!!!
Dan
uwa ina fatan za ka ilmantu da
wannan labari kamar yadda nayi.
ALLAH YASA
MUCIKA DA IMANI, YASA MU DACE DUNIYA DA LAHIRA. AMEEN!
Allah ya sa mu dace, Ya bamu sa'ar rayuwa. Amin
ReplyDeleteAllah ya sa 'yar tafiyar nan ta mu tayi kyau.
Delete