Mulkin
Kasa: Yaushe ya zama gadon ‘Yan Arewa?
An hade Kasar Najeriya ne
fiye da shekaru dari da suka wuce, wannan hadin da Turawa dai suka yi bai wuce
a takarda ba, Inji wani Tsohon Shugaba a Kasar, shi kuwa Sardauna kiran wannan
hadin gambizar ma yayi kuskure. Don kuwa tun a wancan lokaci Najeriya na da
miliyoyin mutane dabam-dabam, akwai kabilu fiye da 200. Sai dai Turawa ba su
damu ba, idan har bukatar su, za ta biya. Daga samun ‘yancin kai a shekarar
1960 zuwa yau (Kusan shekara 56), Arewacin Kasar kadai ta mulki Najeriya na
kusan shekaru 40! Wanda wasu na ganin abin ya zama tamkar dai gadon gidan su!
Hausa-Fulani
a Arewacin Najeriya
Duk da cewa akwai kyakkyawar
alaka tsakanin Hausa da Fulani a Kasar nan, sai dai wannan Kalmar ta
‘Hausa-Fulani’, ‘Yan Jaridun Kudancin Kasar nan ne suka fara kirkiro ta, don
wani burina siyasa. A wajen su duk wanda bai tsallaka gadar Jebba ba, ya zama
Hausa-Fulani; da Banufe, da Babarbare, da Bagwari, da Babushe, da Bakatafe, da
Babole, da Ba’ame da Bagizime duk Hausa-Fulani ne kawai! Hakan zai sa ka
fahimci dalilin da ake kallon Abubakar Tafawa-Balewa, Yakubu Gowon, Ibrahim
Babangida, Sani Abacha, Abdussalami duk a matsayin Hausa ko Fulani (Ko duka,
kamar yadda suka hada)
Mulkin
Mallaka
Lokacin da Turawan Kasar
Ingila na mulkin mallaka suka raba Kasar, sai ya zama Arewa ta fi ko ina girma.
Bari ma, ta fi dukkanin bangaren kudancin Kasar, wasu suna ganin da gan-gan aka
yi hakan. Ko da ma can Turawa ba su mulki Malam Bahaushe kai tsaye ba, sai dai
suka yi amfani da Sarakunan sa. Mafi yawancin mutanen Arewa musulmai ne, kuma
Hausawa (kusan sama da kashi 70 bisa 100), domin addinin musulunci ya shigo
Kasar tun kusan shekaru 500 baya. Yayin da su kuma ‘Yan kudancin Kasar sai suka
rungumi Turawan hannu biyu, da dama suka bar addinin su na gargajiya suka bi addinin
Kiristanci, da ma duk abin da aka yi masu talla.
An yi fafutukar neman
‘Yancin Kasar nan, wanda ya kai aka samu a Ranar 1 ga watan Oktoban 1960 (Abin
da ya sa aka kawo lokacin gaba, domin ‘Yan Arewa ba su shiryawa mulki a okacin
ba). Wani bincike ya nuna cewa bai wuce kashi 2% na ‘Yan Arewa suka san Boko ba
(Duk da cewa sun yi karatun Ajami). Da aka shirya siyasa kuwa, sai Mutanen
Arewa suka kafa Jam’iyyar NPC, A kudu-ta-yamma kuwa a ka shiga AG, ta su
Awolowo, yayin da mutanen su Zik watau Inyamurai suka bi bayan NCNC. Da aka
tambayi Ahmadu Bello game da halin siyasar, sai yace ai tuni zai murkushe su
Awolowo, hakan kuwa aka yi! Duk da cewa ana ganin su koma-baya, amma da yake
abin yawa ake bi, Arewa ta mamaye siyasar Kasar. Ko da yake Jam’iyyar NPC ta su
Sardauna ba ta samu rinjayen da ake bukata ba (amma ta fi kowace Jam’iyya rinjaye
a Majalisa) sai aka shiga hadin-kai da Jam’iyyar NCNC ta su Arzikwe, aka kafa
Gwamnatin hadaka. Arewacin Kasar na mulki, Yarbawa; su Awolowo suna adawa.
Jamhuriya
ta daya
Abubakar Tafawa-Balewa ya
zama Firayim-Minista, shi kuma Nnamdi Arzikwe ya zama Shugaban Kasa (duk da
cewa a suna ne kurum). An ta samun korafai na cin hanci da rashawa daga wajen
‘Yan Siyasar Kasar. An kai ma Balewa kukan satar da wasu Ministoci suke
tafkawa, sai dai abin ya fi karfin sa, domin kuwa idan yayi wani yunkuri,
Gwamnati za ta watse (tun da hadaka aka yi). Bayan an kara gudanar da zabe
Jam’iyyar NPC ta Mutanen Arewa ta kara lashe zaben. Kafin nan an samu rikicin
siyasa ya barke a Bangaren Yarbawa, har ta kai an kafa dokar ta baci, a wannan
yanayi an samu juyin hali. Daga nan wasu suka fara kokarin ganin bayan wannan
Gwamnati.
Juyin
Mulkin farko da na biyu
A watan Junairun shekarar 1966
aka yi juyin mulkin farko a Kasar, wasu (mafi yawancin su) ‘Yan kabilar Ibo
suka hambarar da Gwamnatin Balewa, suka kuma kashe su Sardauna da manyan
Sojojin Arewa. Haka kuma, an kashe wasu kadan daga cikin ‘Yan siyasar kudun
(Irin su Ministan Kudi Festus Okotie-Eboh), amma kusan duk wani Inyamuri da ke
mulki ko gidan Soji ya sha! Masu juyin-mulkin sun yi kokarin kawo sauyi a
Kasar, a cewar su, game da yadda ‘yan siyasa suka shiga facali da dukiyar Kasa
tsakanin su. Sai dai an samu taka masu birki. Wani kuma Inyamurin ne dai ya
dare mulkin Kasar, Shugaban Hafsun Sojin Kasar, Janar Aguyi-Ironsi.
Bayan kisar su Firamiya na
Arewa, Sardauna, kuma Aguiyi-Ironsi ya hau mulki, Hausawa sun ga wulakanci da
muzanci a Kasar. Shugaban Kasan bai kuma dauki wani mataki ga wadanda suka
kashe manyan Arewan ba (Irin su Major Nzegwu, wanda ya zauna gidan Firimiya kuma
shi ya kashe Sardunan). ‘Yan Arewa ba su gama hucewa ba, suka kama Ironsi suka
kashe, sun hambarar da Gwamnatin sa cikin wata shida. Bayan wannan juyin-mulki
na gayya, wani Sojan Arewar ya samu darewa mulkin Kasar.
Mulkin
Gowon da rikicin Biafra
Yakubu Gowon, babban Sojan
Arewa a wancan lokaci, wanda kuma ya taka rawar gani wajen hana juyin mulkin
farko, ya zama Shugaban Kasar, duk da cewa yaro ne shakaf! Sai dai fa hakan bai
yi wa Kanar Ojukwu dadi ba, yana ganin shi ya fi dacewa, Ojukwu mutumin Kasar
Ibo ne.
Bayan Juyin mulkin gayyar da
Hausawa suka yi, Inyamurai sun fara gamuwa da barazana game da rayuwar su a
Arewacin Kasar, kai har ta kai, suka fara tserewa suna barin kayan su. Ganin
hakan ne Ojukwu yaga cewa Shugaba Gowon (wanda haifaffen Kiristan Zariya ne) ba
zai iya kare ran mutanen Ibo ba, don haka ya nemi ballewa daga Kasar Najeriya.
Bayan an-kai-an-komo, aka shiga gwabza yaki na basasa tsakanin Sojojin Ojuwkwu
na Biafra da kuma Sojojin Najeriya. Bayan kusan shekaru biyu da rabi ana
fafatawa, yunwa ta tagayyara ‘ya ‘yan Biafra, Ojukwu ya sulale, aka tsaida
wutar yaki, aka sasanta. Aka dawo kamar dai ba ayi ba!
Wasu Inyamuran dai suna
ganin Sojojin Najeriyar irin su Murtala Muhammad, M. Shuwa, Shehu ‘Yaradua,
Obasanjo, Muhammadu Buhari, Babangida, Sani Abacha sun yi masu kisan gilla ne
kawai don sun nemi su fice su bar Kasar Najeriya.
Abin
da ya biyo bayan yaki
Kasar Biafra ta dawo
Najeriya, ba nan kadai ba, sai da Inyamuri ya zama na biyu a duk Najeriya bayan
wani dan lokaci. Shugaba Gowon yayi kokari wajen gyara barnar da aka yi wa Kasar.
Bayan nan kuma ya kasa cika alkawarin sa na sauka daga mulki. Daga nan ne wasu
Sojojin Arewacin Kasar suka hada kai suka hambarar da Gwamnatin sa yayin da ya
bar Kasar. Murtala ya karbi mulkin Kasar, ya kuma kawo shirin gyara
gadan-gadan, sai kai kafin yayi nisa aka ga bayan sa. Bayan an kashe Murtala
bayan watanni shida da karbar mulki, sai mataimakin sa ya karba, Janar
Obasanjo. Obasanjo yayi kokarin karasa ayyukan Murtala, duk da kuwa cewa
bayarabe ne, wasu na ganin ai ‘Yan Arewa, mataimakan sa, TY Danjuma da Shehu
Yar’adua ne kawai suka yi mulkin. Bayan an yi zabe, Janar Obasanjo ya dauki
mulki da hannun sa, ya mika ga masu farar hula, abin da ba a taba yi ba a
Najeriya, kai! Yammacin Afrika!
An
dawo Mulkin farar hula
Uku daga cikin manyan ‘yan
takarar zaben Shugaban Kasan na 1978, za a iya kiran su Hausa-Fulani (duk da
dai ba haka ainihin abin yake ba). Sauran ‘Yan takarar kuma sune; Zik dai wanda
ya fito karkashin NPP (wanda Jam’iyyar NCNC ce ta rikida) da kuma Awolowa shi
kuma karkashin UNPP (wanda a zahiri, tsohuwar Jam’iyyar AG ce) sai Shehu
Shagari wanda ya lashe zaben a karkashin Jam’iyyar NPN (kusan ace dai tsohuwar
NPC ta su Sardauna ta hada kai da wasu). Wannan karo ma dai su Awo da Zik ba su
samu nasara ba kan Hausawa.
Yarbawa dai musamman, ba su
ji dadin faduwa zaben ba. Sun zargi Janar Obasanjo da Hukumar zabe ta Kasa da
wata manufa, abin har ya kai ga Kotun Koli. Su kuwa Inyamurai sun samu
Mataimakin Shugaban Kasa, Alex Ekwume. Shugaba Shagari yayi kokari wajen samun
daidaito wajen raba dama da duk mukaman Kasa, ya zama ba a cuci dan Arewa ba
nan gaba. Sai dai abubuwa fa sun tabarbare ainun lokacin Shagari, cin hancin da
aka yi da, ya zama wasan yaro. Da aka gudanar da zabe a shekarar 1983,
Jam’iyyar su Shagari ta kara lashewa, sai dai wannan karo, an zuba magudin tsiya!
Soji
Sun dawo!
‘Yan Arewa ne dai suka kara
karbe abin daga hannun ‘dan Arewa; ja ya fado, ja ya dauka! Sojoji ba su yi
nisa can ba a Bariki, bayan da abin yayi kamari sai suka kutso kai! Janar
Buhari ya zama Shugaban Kasa bayan Juyin mulkin Soji. Janar Tunde Idiaghbon ya
zama mataimakin Shugaban Kasar na Soja (Shi ma kuma Musulmi, wasu ma na masa
kallon Bafullatanin Ilorin ba Bayarabe ba). Suka shiga gyaran Kasar musamman
game da harkar cin hanci dsr, tun can an san Buhari da gaskiya da rikon amana.
Gwamnatin Buhari ta shiga kame manyan ‘Yan siyasar Kasar har sai sun kwaci kan
su (musamman na Jam’iyyar UPN da NPN); daga kaji wanda za a daure shekara 150
sai mai 200 a gidan yari. Janar Buhari dai Najeriyar ya sa a gaba; Buhari ya
bindige ‘yan fashi da makami da masu cinikin kwayoyi, ‘Yan Jaridu ma sun ga ta
kan su a wannan mulki!
Zamanin
Babbangida
Ba a cika watanni ashirin
ba, wasu daga cikin na kusa da Janar Buhari suka hambarar da shi, su ka kuma
garkame shi. Har wa yau kaji, wani dan Arewar ne dai ya kara karbe mulkin
Kasar, Janar Ibrahim Babangida. IBB ya dade yana mulki, ya kawo cigaba musamman
na tituna da sauran gine-gine a zamanin sa a Kasa baki daya, ya kuma karbo
bashi daga Yamma (abin da Buhari ya ce a’a). IBB mutumin Jihar Neja, ya kirkiro
sabbabin Jihohi a Kasar, ya kuma saki duk wadanda Buhari ya daure, wadansu kuma
aka rage wa’adin zaman na su a yari.
A shekarar 1990 aka ga dai
cewa IBB ba sa da ranar sauka daga mulki, wani daga cikin Sojojin Kasar ya
shirya kifar da Gwamnatin! Manjo Okar (wanda Mutumin Kudancin Kasar ne) yace
yaga alama cewa ‘Yan Arewa sun dauki mulkin Kasar gado, abin da suke so, su yi
ta mulkar sauran (Kudanci da Tsakiya) ‘Yan Kasar… Manjo Gideon Okar ya shirya
hambarar da Gwamnatin IBB ya kuma hana ‘Yan Arewa Shugabancin, sai dai an ga
bayan sa, hakan dai ya faru da wani babban Soja kuma aminin Shugaba IBB watau
Mamman Vatsa.
A zamanin IBB Najeriya ta
shiga cikin tawagar Kasashen musulunci watau IOC a boye. A lokacin ne kuma aka
soke zaben Abiola, bayan alamu sun nuna cewa ya buge Bashir Tofa (Mutumin Kano,
Hausa-Fulani) war-was! Hakan dai ta sa ba girma, ba arziki, IBB ya bar mulkin.
Daga
Shonekan zuwa Abacha
IBB ya mika mulkin Kasar ga
Gwamnatin rikon kwarya ta Cif Shonekan, shi Ernest Shonekan dan kasuwa ne a
Legas. Kafin a fahimci alkiblar Kasar, tuni Janar Sani Abacha ya kara juya
mulkin. Wasu da dama sun ce da gan-gan Janar IBB ya bar Janar Sani Abacha a
Gwamnati, shi kuwa dai yace sam ba haka abin yake ba.
Janar Abacha ya rusa
Majalisu da duk wani tsarin Damokaradiyya na Kasar, yayi kokarin hada taron
ganin inda Kasar ta dosa. Daga nan kuwa dai ya shiga kama wasu tsofaffin
Sojojin Kasar (Har da irin su Janar Obasanjo da Yaradua, wanda sun rike mulkin
Kasar). Janar Abacha kuma ya kama Abiola bayan ya bayyana kan sa a matsayin
Shugaban Kasa. Zamanin Abacha ya murksuhe mutanen yankin Ogoni. Janar din ya
hada kai da Shugaba Gaddafi na Kasar Libiya har Najeriya ta shiga sahun wasu
Kasashe 8 masu tasowa. Abacha ya zama gagarabadau, sai da ya kai dai Turai tayi
baran-baran da Abacha. Kwatsam! Sai ya mutu! Wasu dai na ganin ya gyara
tattalin arzikin Kasar a lokacin sa, ana dai zargin kuma cewa ya saci kudi na
hauka a Gwamnati!
Abdussalami
ya dawo da farar hula
Bayan mutuwar Abacha,
Shugaban Hafsun Soji na Najeriya, Janar Abdussalami Abubakar yayi maza ya haye
mulkin. Sai dai yayi alkawarin dawo da siyasar damukaradiyya Kasar, hakan kuma
yayi, bayan shekaru ashirin ana fama da masu khaki. Sai dai mutane da dama har
da irin su Babban Lauyan nan, Gani Fawahemi ya kai karar Shugaban Kasar, saboda
yadda aka rika gudanar da mulkin Kasar na dan wannan lokaci, an maida Inyamurai
saniyar ware. Manyan Hukumomi da ma’aikatun Kasar irin su; NPA, NNPC, NEPA, FSC,
NIS, NPS, NITEL, dsr duk suna hannun Hausa-Fulani.
Obasanjo
zuwa Yaradua da Jonathan
A 1999 aka gudanar da zabe,
Obasanjo, bayan ya fito daga gidan yari ya lashe zaben, ya buge wani bayaraben
watau Cif Olu Falae. Wasu na tananin cewa yarjejeniya ce aka yi na zai mika
mulki ga Hausa-Fulani idan ya kamala wa’adin sa (ko dama dai IBB zai so ya
fanshe kan sa daga maganar soke zaben Abiola wajen yarbawa). Ko da Obasanjo
yaji dadin mulki, sai yayi mursisi, har ya nemi tazarce na uku. Da wannan
yunkuri bai yiwu ba, sai ya kakaba Ummaru ‘Yaradua da mataimakin sa Goodluck
Jonathan.
Ummaru ‘Yaradua Hausa-Fulani
ne (Danuwan Aminin Obasanjo, Shehu ‘Yaradua) shi kuwa bai taba sa ran mulkin
Kasar ba, bayan ya kamala Gwamna a Jihar Katsina, ya zama shugaban Kasa a 2007.
Ya buge wasu manyan ‘Yan takara duk ‘Yan Arewa; Atiku Abubakar na AC da Muhammadu Buhari na ANPP a Jam’iyyar
su ta PDP. An dai tafka magudin da ba a taba irin sa ba a wannan zabe, da bakin
sa, sai da ya fadi kusan hakan.
Yar’adua yayi kokarin kawo
sauyi a Arewa da ma Najeriya sai dai ya samu matsalar tattalin arziki na duniya
da rashin lafiyar da ta ci karfin sa. A lokacin nan mataimakin na sa Goodluck
Jonathan, bai san abin da yake faruwa ba, asali ma ‘Yaradua ya wuce asibiti ba
tare da ya bar mukaddashi ba. Wasu masu kishin Kasar (har da ‘Yan Arewa) su ka
matsa, har sai da aka nada Jonathan rikon kwarya. Bayan ‘Yaradua ya rasu a
watan Mayun 2010, aka tabbatar da Jonathan Goodluck Shugaban Kasan Najeriya.
Jonathan na hawa, ya kafa
Gwamnati, ya kuma tsaida wasu ayyukan da Marigayi ‘Yaradua ya fara a Arewan da
fadin Kasar. Bayan ya kare wa’adin ‘Yaradua, ya nemi tsayawa takarar kan sa,
wanda ya saba yarjejeniyar jam’iyyar PDP ta kama-kama. Haka kuwa yaci zaben, ya
buge wasu ‘Yan Arewa, irin su Muhammadu Buhari dai na CPC, Nuhu Ribadu da
Ibrahim Shekarau. Sai dai a lokacin sa rikicin Boko Haram yayi kamari kwarai,
mutane dubannai suka rasu, wasu kuma da dama suka gudu ko aka sace su. Cin
hanci da masifaffiyar sata a Kasar ya zama abin ba a Magana kawai! Hakan dai ta
sa aka zabi Muhammadu Buhari.
Muhammadu
Buhari
Wanda ake yi wa lakabi da na
talawa, Buhari yayi mulki a baya, ya kuma nemi ya dawo har karo uku. Ya samu
nasarar buge Shugaban Kasan da ke ci bayan sun kafa Jam’iyyar hadaka (tsakanin
‘yan adawa). Buhari dai ya tsaida rikicin Boko Haram da ke kashe mutane da
sunan addini da hawan sa. Sai dai yanzu Kasar, musamman Arewa ana fama da
matsalar yunwa da rashin kudi a kasa. Shugaba Buhari dai yace dole a koma noma
a Kasar domin samun abinci. Tuni kuma Shugaba Buhari ya bada umarnin a fara
nemo mai a Yankin Arewan.
Wasu kuwa suna ganin Shugaba
Buhari wanda Hausa-Fulani ne na neman ganin bayan su; ko ta hanyar Makiyaya ko
ta wata hanyar dabam. Su kuwa ‘Yan yankin Neja-Delta masu arzikin mai, tuni
suka shiga barna, suna fasa butatan Kasar. Shugaban dai yace ko su ji su daina,
ko jikin su ya fada masu. A mulkin sa an rufe irin su Sambo Dasuki (Su Dasuki
ne suka kifar da Gwamnatin Buhari a 1985) da zargin satar kudin makaman Kasar,
haka kuma ana daure da Shugaban Shi’a, Ibrahim Zakzaky da kuma Shugaban
Kungiyar IPOB ta Biafra, Nnamdi Kanu, wata da watanni.
Tsohon
Shugaban Kasa Jonathan tare da Shugaba-na-yanzu, Muhammadu Buhari
A
karshe…
Wasu dai suna da ra’ayin
cewa ‘Yan Arewa ko dai Hausa-Fulani sun dauki mulkin Kasar kamar gado, su kadai
suka iya! Duk da wasu na ganin ‘yan Arewa a matsayin koma-baya ko kuma
ci-ma-gari-banza; sai dai a hako mai a Kudancin Kasar, a ba su, a bulus. Mafi
yawancin wadanda suka mallaki rijiyoyin mai a Kudancin Kasar, ‘Yan Arewan ne. A
baya, an koka da yadda Hausa-Fulani su ka mamaye gidan Sojin Kasar da ma
Hukumar ‘Yan Sanda. Har yanzu dai wasu na kukan cewa Hausa-Fulani suna murkushe
su. Hakan dai ya sa wasu ke kururuwar Biafra har wa yau. Sai dai kusan gaskiyar
maganar ita ce, masu mulki duk suna murkushe mu gaba daya a sama.
Muhammad Malumfashi ya rubuta wannan a shafin NAIJ Hausa domin tunawa da Ranar
Yancin kan Najeriya.
@Ya_waliyyi
@Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment