‘Yan Kwankwasiya sun ce za su kai Ganduje Kotu idan bai cire masu hula ba
– ‘Yan Kwankwasiyya sun kira Gwamna Abdullahi Ganduje da ya tube masu Jar hula ko kuma su kai sa Kotu
– Kwankwasiyya sun ce Ganduje ya bar akidar don haka babu dalilin cigaba da zama da alamar su
– Rikicin Ganduje da Tsohon mai gidan na sa Kwankwasiyya na ta kara cabewa
A jiya DailyTrust ta rahoto
cewa magoya bayan Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ‘Yan kwankwasiyya’ sun nemi Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kanon da
ya tube jar hular da ke kan sa, idan ba haka ba kuma za su shiga Kotu da shi
nan da kwana biyu.
‘Yan
Kwankwasiyya sun ce Gwamna Ganduje ba ya tare da su cikin tafiyar, don haka
babu dalilin cigaba da saka jar hular Kwankwasiyya. A jiya ne dai Tsohon
Gwamnan Kano kuma Shugaban tafiyar Kwankwasiyya Amana Injiniya Rabiu Musa
Kwankwaso ya cika shekaru 60 a duniya.
Haka kuma tafiyar
Kwankwasiyya ta cika shekara 6 kenan a duniya, a wajen bikin murnar cika
shekarun Tsohon Gwamnan kuma jagoran tafiyar ne wani mabiyin Kwankwasiyya, kuma Shugaban Hannun karba-Hannu
badawa, Alhaji Sharu Gwammaja yace dole fa Gwamna Ganduje ya cire jar hula tun
da yanzu ya baude. Alhaji Sharu Gwammaja yace sun ba Gwamnan awannin 48 da ya
cire hular ko su shiga Kotu
‘Yan Kwankwasiyya sun ce Ganduje
nacin alfarmar jar hula wajen mutanen Kano, duk cewa ba dan ta bane. ‘Yan
Kwankwasiyya sun ba mutanen Kano hakuri da suka tsaida masu Ganduje a matsayin
Gwamna, suka ce ai an kuma gama.
A Karanta sauran manyan labarai na Kasa a shafin NAIJ Hausa
@Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment