Sakin ‘Yan Matan Chibok duk rudun banza ne Inji Gwamna Fayose
– Gwamna Fayose na Jihar Ekiti yace sakin ‘Yan Matan Chibok dinnan duk hanyaniyar banza ce kurum
– Gwamna Fayose yace ana nema ne a kauda kawunan mutane daga matasalar tattalin arzikin Kasar da ake fama da ita
– A jiya ne aka saki wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok da aka sace fiye shekaru biyu da suka wuce a Jihar Borno
Gwamnan Jihar Ekiti Ayo
Fayose yace bai ga abin farin ciki ba da Gwamnatin Kasar ke yi na kubuto da
‘Yan matan Chibok da aka sace shekaru fiye da biyu da suka wuce. Gwamna Fayose
yace wannan kawai kokarin kauda hankalin ‘Yan Najeriya ne daga halin da ake
ciki a fadin Kasar.
Gwamna Fayose yace kubuto da
wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok ba zai canza wahalar da ‘Yan Najeriya suke
sha ba a Kasar nan. Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose yace mafi damar ‘Yan
Najeriya suna fama da wahala a halin yanzu.
Gwamnan Jihar Ekiti Ayo
Fayose yace ba abin da ‘Yan Najeriya za su iya sai addu’a ko Ubangiji ya kawo
saukin wannann wahala da ake fama da ita. Gwamnan Fayose yayi wannan magana ne
jiya a Garin Iyin-Ekiti da ke Karamar Hukumar Ifelodun/Irepodun yayin da yake
bude wasu ajijuwa. Fayose yace ba ta ‘Yan matan Chibok ake ba, yanzu yunwa ake
fama da ita.
KU KARANTA: Cikakken labarin a shafin NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment