Thursday, October 20, 2016

Lionel Messi yayi watsa-watsa da Guardiola



Dan wasa Lionel Messi ya zubawa Man City kwallaye uku



Lionel Messi ya durawa Kungiyar Man City kwallaye uku a wasan Uefa Champions League

 

Barcelona ta zazzagawa Man City kwallaye hudu da nema 

 

Pep Guardiola ya hadu da Tsohuwar Kungiyar sa

 





A daren jiya ne Kungiyar Man City ta Pep Guardiola ta sha kashi hannun Tshuwar Kungiyar sa, Barcelona. Barcelona ta jibgawa Kungiyar Man City kwallaye hudu da nema a Gasar Uefa Champions League ta Nahiyar Turai.

Pep Guardiola dai bai ji dadin dawowa Kungiyar ta sa ta da ba, Dan wasan da y arena Lionel Messi ya jibga masa kwallaye uku watau hartrick a wasan da aka buga a Filin Camp Nou da ke Barcelona ta Kasar Spain. 


Messi kadai ya zuba kwallaye uku a ragar Tsohon Golan na sa, Carlos Bravo. Kafin a tashi wasan dai Gola Bravo ya samu jan kati, haka ma kuma Dan wasa Mathieu na Barcelona ya sha jan katin a wasan. Dan wasa Neymar ne ya ci kwallo ta hudu a wasan. An dai tashi da ci hudu da nema.



Twitter: @Ya_waliyyi

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...