Wednesday, October 5, 2016

Shugaban Kasa Buhari ya fara aika takardun kasafin kudin 2017 zuwa Majalisa


Muhammadu Buhari ya aika da takardar kasafin kudin shekara mai zuwa


Reuters ta rahoto cewa har Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya fara aikawa da takardun kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2017 zuwa Majalisar Dattawa ta Kasar. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika takardar da za a duba kasafin kudin shekara mai zuwan ne domin a amince.
Wannan takarda tana dauke da yadda Najeriya za ta kashe kudin ta shekara mai zuwa, har sai Majalisar dattawar Kasar ta amince sannan za a kawo ainihin kundin kasafin kudin shekara mai zuwan ta 2017.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya aika da kasafin kudi Majalisa
Takardar ta nuna cewa Najeriya za ta kashe Fiye da Tiriliyan shida da biliyan dari takwas, 6.86tr watau dala biliyan $22.57 a shekara mai zuwa. Wannan kudi dai ya ma fi na bana da aka lissafa Tiriliyan 6.06. Najeriya dai ba ta taba kasafin irin wannan makudan kudin ba a Tarihi.
Tattalin arziki Najeriya dai ya ruguje bayan karyewar darajar mai a duniya, haka kuma Kasar ba fama da Tsagerun Neja-Delta wanda suke fasa butatan man Kasar, don haka gangan man da Kasar ta ke fitarwa sun ragu sosai. An dai kiyasta gangar mai a kan $42.5 a kasafin na 2017, da kuma $1 a kan N300.2500.

Ga shi ma dai kuma Hon. Jibrin ba ya nan.

Muhammad Malumfashi ya rubuta wannan rahoto a shafin NAIJ.com

Domin karanta wasu labaran sai a garzaya shafi na na NAIJ Hausa: https://www.naij.com/author/muhammad-malumfashi.html

 Twitter: @ya_waliyyi


 


No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...