Friday, October 14, 2016

Motar Duniya



DUNIYA MOTA

Duniya shiga dakin mota; shiga da kai, fitowa da baya…-Mawaki Alhaji Sani Sabulu

Wani mutum ne yashirya yin wata tafiya. Ya dauki matarsa da ’ya’yansa cikin motarsa suka kama hanya. Ba su yi nisa ba suka hadu da wani mutum tsaye a bakin hanya. Ya daga musu hannu suka tsaya, ya nemi su dauke shi. Maigida ya tambaye shi: “Wane ne kai?” Ya ce, “Ni ne dukiya.” Nan take iyalin suka dau shewar cewa ga abokin tafiya, maganin takaicin duniya. Suka ce lallai a dauke shi su tafi tare. Dama motar irin babbar Jif din nan ce mai yalwar mazaunai wato (family car), sai suka dauke shi suka tafi. Suna yin gaba kadan sai suka tarar dawani mutumin, shi ma a bakin hanya yana dagamusu hannu, sai maigida ya tsaya. Ya tambaye shi: “Wane ne kai?” Ya ce: “Ni ne sarauta da matsayi.” Iyalan na jin haka suka ce a dauko shi. Domin babu abin da yin sa zai gagarimutum a duniya, muddin yana da sarauta da matsayi. Shi ma suka dauke shi suka wuce. Suna kara gaba kadan sai ga wani mutumin tsaye a gefen hanya, shi ma ya daga musu hannu suka tsaya. Maigida ya tambaye shi: “Wane ne kai?” Ya ce: “Ni ne Addini.” Maigida ya waiwayi iyalansa, sai ya ga sun yi jugun-jugun cike da damuwa. Tun kafin ya nemi shawararsu suka ce: “Wannan ba abokin tafiya ba ne. Takura mana zai yi da hukunce- hukuncensa na halal da haram,ya hana mu more rayuwarmu. Ya dai jira nan gaba ma dawo mu dauke shi bayan mun gama more jin dadin rayuwarmu.” Maigida ya yarda da shawarar iyalansa, suka wuce suka bar Addini nan tsaye, suna taQama da wadatar dukiya da alfarmar sarauta da matsayi, har suka ci karfin tafiyar daza su yi.
Suna cikin tafiya sai suka iso wani wurin binciken ababen hawa (Cheking Point). Suka tsaya don suma a duba su. Sojan da ke bincike yace da maigida: “Kai fito mu tafi, tafiyarka ta kare daga nan!” Maigida ya ce: “Kai kuwa wane ne kai?” Yace: “Ni ne mala’ikan mutuwa.Ina bincike ne a kan addini. Kai kuwa ba ka da shi.” Maigida ya ce: “Affff", ai na baro shi a hanya. Bari na koma na dauko shi.” Mala’ikan mutuwa ya ce: “Ai wannan damar ta wuce ka har abada!” Maigida ya kara cewa: “To ai ina tare da dukiya da sarauta da matsayi da dukkan iyalina.” Mala’ikan ya ce: “Ai duk wadannan ba za su amfane ka da komai ba. Addini kadai ake bukata a nan.” Maigida ya waiga sai ya ga matarsa ta haye mazauninsa na direba, ta ja mota sun yi tafiyarsu ita da sauran iyali tare da dukiya da sarauta da matsayin. Suka bar shi nan mala’ikan mutuwa ya tasa keyarsa. Babu iyali! Babu dukiya!! Babu sarauta da matsayin!!!

Dan uwa ina fatan za ka ilmantu da wannan labari kamar yadda nayi. 

ALLAH YASA MUCIKA DA IMANI, YASA MU DACE DUNIYA DA LAHIRA. AMEEN!

2 comments:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...