Hukumar Jarrabawar JAMB ta kashe amfani da kati 'Scratch Card'
– JAMB ta kashe amfani da kati wajen jarrabawa a Kasar
– Hukumar tace tuni an daina yayin wannan tsari
– JAMB din ta kuma bayyana cewa akwai rashin gaskiya a shirin
Hukumar Jarrabawar JAMB ta
kashe amfani da kati a fadin Kasar kamar yadda aka saba. Shugaban Hukumar
Jarabawar JAMB din Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana haka a wannan makon. Ishaq
Oloyede yace daga yanzu ba za a kara amfani da katin nan ba wajen rajista ko
makamancin sa.
A baya dai JAMB din tana
saida wani kati ne wanda ake amfani da shi wajen Rajista da kuma duba sakamakon
Jarabawar ta shiga Jami’a. Sai dai Yanzu Hukumar ta JAMB ta kashe wannan tsari,
tace akwai badakala a ciki.
Hukumar ta JAMB
ta sanar da hakan ne ta bakin mai magana da yawun ta a wajen wani taro da
Shugabannin Jami’a a Abuja. Hukumar Jarabawar JAMB din na ganin akwai hanyoyin
cuwa-cuwa ta tsarin katin nan, hakan ta sa aka kawo wani sabon tsari da ake
kira PIN.
Har wa yau Ishaq Oloyede ya
kira Gwamnati da ta koma yadda aka saba a baya, watau nada Tsofaffin
Shugabannin Jami’o’i a matsayin wadanda zasu rike Hukumar JAMB din ta Kasa.
Haka kuma Majalisar Dattawar Kasar ta kara wa’adin Jarabawar zuwa shekaru uku.
A baya dai Gwamnatin Kasar ta soke Jarrabawar Post-UTME da ake yi wajen shiga makarantun Jami'a.
A Karanta cikakkun labarai a NAIJ.com
Twitter: @Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment