Wednesday, October 12, 2016

China za ta aika Tsohon dan wasan Kwallon kwando zuwa Duniyar Mars


Kasar China ta nada Jakada zuwa duniyar Mars


 
Kasar China ta nada wani Tsohon dan wasan kwallon kwando a matsayin Jakadar duniyar Mars mai suna Yao Ming. Yao-Min ya bugawa Kungiyar kwallon Kwandon Houston Rockets lokacin da yake buga wasa.

Ban da kuma dan wasa Yao Ming Kasar China ta zabi wasu mutane goma kuma dabam a matsayin Jakadun Kasar zuwa duniyar ta Mars. Kasar China na kokarin aika jirgin satalai na sama jannati zuwa duniyar ta Mars nan da shekarar 2020. 


Nan daa shekarar 2020 Kasar China na shirin aikawa da jirgi zuwa duniyar ta Mars wanda ke kusa da duniyar nan ta mu. Wannan jirgi dai zai rika amfani da karfin rana ne wajen aiki. Bayan tsohon dan wasan kwallon kwandon, Kasar China ta zabi wasu mutanen kuma a matsayin jakadun na ta, sun hada da; wani marubuci mai suna Liu Xing, da wata matashiyar ‘Yar wasar Kwallo mai suna Lang Ping.

Duniyar Mars ce mai makwabtaka da mu, sai dai dabam ta ke da ta Dan Adam, duk akwai alamun rayuwa da fitowar tsirrai, duniyar na da matukar kura. Kasar China na ta kokarin kafa tarihi a wannan fage na ilmin.

A shekarar 2020 ne kuma ake sa ran Kasar Najeriya.... za ta fara kera fensiri.





Muhammad Malumfashi ya fassara wannan rahoto
Twitter; @ya_waliyyi



No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...