Sunday, October 16, 2016

Wakar Mutuwa

Wakar Mutuwa; Muhammad Malumfashi



Mutuwa daya ta,
Sanadi a' kala-kala,
Kabari kowa da nasa,
Tambaya dole ka amsa,
Idan kayi gardama, ko kaci jibga,
Munkar-Nakiru na nan, masu guduma,
Ban da maciji, ga kunama, 
Daga barzahu, sai Kiyama,
Filin tonon silili da gaskiya, 
Ranar da babu karya,
Kowa na tube, Iko sai ga Jalla,
Ko ka ga Sarkin kasar ku? Yana nan haihuwar uwar sa,
Can a samu Muhammadu (SAW) ya roko alfarma,
Bayan yayi kirari ya jinjina ma Tabara,
Sai Hisabi awo na mizani, babu cuta,
Kowa na ta kan sa,
Idan ka cuce wani ne sai a rama,
A diba ladan ka duk a ba sa,
Idan babu ladar dada, zunubi nasa sai a dibo a jibga,
Babu ruwan uwa da danta,
Ko wani miji da yar matar sa,
Sai dai bawa da ayyukan sa,
Gidaje biyu, Aljanna ko wutar ubangiji Ta'ala
An ce Allaah kadai ya san namijin kabewa, 
Fatar mu ace takarda a hannun dama an ka mika, 
Mai hannun hagu sai ka ji yana, ai mu har yanzu da saura jama'a,
Allah kiyaye bawa da jahannama,
Ranar wuta tana ta kugi, za ta fusga,
Mummuna ce baka, don azaba,
Ita ko aljanna, gidan ni'ima don a wala,
Allah ya samu cikinta,
Ni ko dan matan cikin ta,
Ga koramu na ta gudana
Ga giya sai mu taba, ni yar 'Star' babba za ni kurba,
Ba wani bawali, ba zagayawa,
Ba a koshi, kuma babu yunwa,
Da ka yi marmari sai a ba ka,
Karshe zad dadi sai a ga Allah ta'ala,
Can wuta ko, ko ruwa ka nemi a ba ka,
Na kwata ne, ga zafi ya dalma,
Ya huda makwogwaron, don tafasa,
Ga doyi, wari ba a ma magana,
Ina ma abinci, mai huda tumbin yan Jahannama,
Ga shi ba dama a koma duniya, 
Ko ace an mutu don a huta,
Siradi muminai za su tsallaka,
Wani kamar walkiya, wani kamar ya fada,
Da kyar na sha ai yafi da kyar aka kama,
Allah dai ya sa abin ya zo da sauri ya kiftawa,
Ran sarki ya dade, ai ba ya hana Mutuwa,
Ga mai nakuda, ta zo za ta haihu, ran aka dauka,
Jinjiri ya leko, uwar sai ta koma,
Haka yar kanwata Amina, yanzu sai ace marigayiya,
Ba ruwan mutuwa da wai ko karama ce, 
Shege! Cinnaka, ba ka san na gida ba,
Wata rana iyayena za ta dauka,
Allah ya jikan su ya sa su huta,
Allah kai ni Madina nima,
In mutu can ina mai Salla,
Masallacin shugaban mu nayi sujuda!

امين

Twitter: @ya_waliyyi





2 comments:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...