Monday, October 24, 2016

A.B.U Zaria za ta ja wutan lantarki daga bola da ba-haya

Jami’ar ABU Zaria za ta samar da 1.2MW daga ba-haya


 

Jami’ar Ahmadu Bello University ta Zaria za ta samar da wutan lantarki daga dattin bola

 


ABU Zaria za ta hada kai da wani Kamfanin Kasar waje wajen jan wutan lantarki daga bola

 


Jami’ar za ta samu kusan megawatt daya ta bola da kuma bayan-gida





Shugaban Jami’ar ABU Zaria, Farfesa Ibrahim Garba ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewa Jami’ar ta ABU Zaria na shirin jan wutan lantarki daga dattin bola da ake samu a gonaki da gidaje. Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana wannan ne a farfajiyar makarantar da ke Samaru-Zaria.

Farefesa Garba yace Jami’ar za tayi haka ne domin kudin da ta ke kashewa a wajen shan wutan lantarki yana da matukar yawa, Jami’ar ABU Zaria tana dai kashe akalla Naira Miliyan 86 kowane wata wajen biyan kudin wuta kadai, wanda kuma ba za ta iya cigaba da biya ba Inji Farfesa Ibrahim Garba.

Jami’ar za ta hada kai da wani Kamfanin Kasar Hungary mai suna Agrar-Biothanal, wajen gina mabubbugar wuta daga dattin bolar da ake samu daga gonaki da kuma sauran wurare irin su ba-haya. Idan har an kamalla wannan aiki, Farfesa Garba yace za a samu kusan lita miliyan uku na Sinadarin Ethanol, da kuma ruwan taki fiye da ton dubu, sannan da megawatt 1.2 na lantarki.

Jakadan Kasar Hungary a Najeriya, Farfesa Temak Gabor yace dole Najeriya ta fara neman wasu hanyoyin samun wutar lantarki saboda yawan da ta ke da shi. Makon baya ne dai Gwamnatin Kano da Kaduna suka hada kai wajen irin wannan aiki na samun wutan lantarki.


Muhammad Malumfashi ya fassara wannan rahoto a NAIJ Hausa

Twitter: @Ya_waliyyi
 

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...