– Ana ta kukan cewa wasu mutane sun rike madafan iko a Gwamnatin Baba Buhari
– Ko su wanene wadannan mutane da ba a san su ba?
– Kwanaki dai har sai dai matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta koka a Gidan BBC
Kwanakin baya, Matar
Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta koka da yadda wasu mutane da ba ayi yakin zabe
da su ba suka rike madafan iko a Gwamnatin mai gidan ta a Gidan BBC. Haka ma
Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya taba cewa wasu sun karbe madafan
iko daga hannun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Ko su waye wadannan mutane? NAIJ
sun cinko mutane 6 da ake zargin su su ke rike madafan iko a Kasar a halin
yanzu.
MAMMAN DAURA
Mamman Daura ya zama tamkar
Mataimakin Shugaban Kasa, ko da bai da wani takamamen Ofishi, yana cikin
wadanda suke rike da madafan iko a Kasar. Ko a lokacin da Buhari yayi mulkin
Soja, da shi aka dama. Shugaba Buhari kawu yake a wurin sa, duk da Mamman ne
babba.
ABBA KYARI
Shugaban ma’aikatan Gidan
Gwamnati, Abba Kyari. Tsohon dan tafiyar Buhari ne, ya rike makamai da dama, tun zamanin Gawon ake damawa da shi.A da har ana rade-radin an dakatar da shi daga aiki, sai ga shi kwatsam Ranar Jumu'a a Ofis, ashe hutu ya tafi.
BABACHIR DAVID LAWAL
Sakataren Gwamnatin Tarayya,
Babachir yana daya daga cikin wadanda suke rike da madafan iko a Kasar nan,
kuma ba ya shakkan hakan. Shugaba Buhari na jin ta bakin sa.
Wasu Ministoci
Wasu daga cikin Ministocin
Gwamnatin sun zama masu fada a ji a Gwamnatin Buhari da kuma Jam’iyyar su ta
APC. Wadannan Ministoci da suke da ta cewa a Majalisar zartarwar Tarayya kuwa
sune Tsohon Gwamnan Legas da na Rivers; Babatunde Raji Fashola daRotimi
Amaechi, watau Ministan Sufuri da kuma Ministan Wuta, Muhalli da Ayyuka na
Kasar.
ISMA’IL FUNTUA
Ko da yake ba kowa ne ya ma
taba jin sunan wannan mutumi ba, amma kamar Mamman Daura yana daga cikin
mutanen da suke rike da madafan iko a Kasar nan. Isma’il Funtua, aminin Buhari
ne yana kuma da ta cewa a tafiyar Gwamnati; yana cikin masu fadawa Shugaba
Buhari wadanda za ya nada a Gwamnatin sa
TY Danjuma
Theophilus Yakubu Danjuma,
wanda yana cikin manyan Kasar nan. TY Danjuma mai gidan Shugaba Buhari ne tun a
Soja da kuma Gwamnati, har yau kuma yana girmama sa. TY dajuma tsohon Janar ne,
yana cikin wanda suka yi wa Shugaba Buhari yakin cin zabe. TY Danjuma yayi
sanadiyar nada wasu Ministoci da masu manyan mukamai cikin Gwamnatin Buhari.
Muhammad Malumfashi ya fassara wannan a NAIJ Hausa: https://www.naij.com/author/muhammad-malumfashi.html
Muhammad Malumfashi ya fassara wannan a NAIJ Hausa: https://www.naij.com/author/muhammad-malumfashi.html
No comments:
Post a Comment