Dalilan da suka sa dan wasa Emmanuel Adebayor ya musulunta
– Dan wasan kwallon kafar nan, Emmanuel Adebayor ya bayyana abin da ya sa ya shiga Addinin musulunci
– Emmanuel Adebayor yace ya gane cewa Musulunci shine addinin gaskiya ko a cikin littafin bible
– Fitaccen dan kwallon yace ya fahimci cewa Musulmai sune asalin mabiya Yesu Almasihu
A kwanakin baya can, an
bayyana cewa Fitaccen dan wasan kwallon Kafar nan Emmanuel Adebayor ya bar
addinin Kirista, Emmanuel Adebayor ya musulunta, ya kuma bayyana dalilan da
suka sa ya shiga wannan addini na Islama. Emmanuel Adebayor yace ya gane cewa
Musulmai ne asalin mabiya Yesu Almasihu
AS.
·
Tsohon dan kwallon na Arsenal yace Littafin Bible ya tabbatar da cewa Ubangiji daya
ne a Surar Mark ta 12 Aya ta 29 da wasu wuraren, Musulmai ma suna bautar Allah
daya (4: 171)
·
Yesu AS ya haramta
cin Alade a Surar Leviticus a Aya ta 7, haka Islama ya haramta a Sura ta 6: 145.
·
Yesu AS ya kan ce
Idan Allah ya yarda, haka Musulmai na cewa In shaa Allah. (Sura ta 18: 23-24) kafin
su aikata kowane irin abu.
·
Kuma Yesu AS
na yin Sallama ga mutane kamar yadda musulmai ke cewa Amincin Allah a gare ku
watau Salam Alaikum. (John 20: 21)
·
Bible ya koyar da
wanke fuska da hannuwa kafin ayi Sallah, kamar dai yadda musulmai ke alwala ko
taimama.
·
Hatta Sallar ma da musulmai ke yi, haka ya zo a
Littafin bible (Mathew 26: 39) ake
sallah, watau a fadi da kai ayi Sujuda.
·
Yesu AS na barin gemu
kamar yadda Musulunci ya koyar, haka ita kuma Mahaifiyar sa Nana Maryama AS
tana lullube jikin ta, kamar dai yadda ya tabbata a cikin Genesis , Timothy da
Corinthians da kuma Qur’an 33:59.
·
Yesu AS na yin azumi
na kwanaki kusan 40 a jere (Exodus 34: 28) dsr, Musulmai kan yi azumin Ramadana
su kuma daura da wasu kari bayan nan.
·
An yi wa Yesu AS
kaciya lokacin yana kwana takwas a duniya (Luke 2: 21), kamar yadda aka yi wa
Annabi Muhammadu SAW (Sahih Bukhari, Muslim da Ahmad)
·
Yesu AS da kan say a
kira Ubangiji da suna ‘Elah’ watau kamar dai ‘Allah’da larabci.
M. Malumfashi ya fassara wannan rahoto a NAIJ Hausa
@Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment