NAJERIYA TA DAWO TA DAYA A TATTALIN A ARZIKI AFRIKA
Kula da tafiyar hawainiyar da tattalin
arzikin Najeriya take yi, kwatsam sai ga hukumar bada lamuni ta Kasa wato IMF
ta fito ta ce Tattalin Arzikin Najeriya shine mafi girma a nahiyar Afrika, amma
abin ban al’ajabin shine, wata biyu baya wannan dai hukumar tace tattalin
arzikin Najeriya ya koma na biyu a Afrika
wato bayan kasar Afrika Ta Kudu, ba shakka wannan rahoton ya jawo kace-nace a Najeriya,
shiyasa babban dan kasuwar nan na Najeriya wato Aliko Dangote ya fito yace shi fa
sam bai yadda cewa tattalin arzikin Najeriya ya koma na biyu a Afrika ba, yace
idan ka lura da girman kasar da irin kudaden da ake juyawa, yace zai wuya ace
wai wata kasa ta wuce Najeriya a girman tattalin arziki a nahiyar Afrika. Toh
masana dai suna ta bayanin abinda ya jawo hakar, wato yadda cikin kankanin
lokaci ita hukumar bada lamunin tai amai ta lashe, turkashi, jama’a dai sunata
tofa albarkacin bakin su, wasu suna ganin cewa da gangan ita hukumar tai hakan
don su ciwa Najeriya mutunci a idon duniya, wasu kuma suna ganin cewa inaa, ai
ita hukumar tana anfani ne da bayanai da alkaluma da take da shi kan Kasashe
wajen fitar da irin wannan bayanan, saboda haka bakada hujjar da zaka zargesu
da yin ba daidai ba.
Ita Hukumar Bada Lamunin tace bayan an
kara lissafi akan alkalumar tattalin arziki wadda ya fito a watar Agusta ya
nuna cewa Tattalin Arzikin kasar Afrika ta Kudu nada nauyin Dalar Amurka
biliyan dari uku da daya, ita kuma Najeriya tana da dalar Amurka biliyan dari
biyu da casa’in da shidda (idan aka kula da darajar musayar kudi) wannan
rahotan ya fito ne a watar agusta na wannan shekarar.
Amma kuma sabon kintace da Hukumar Bada
Lamunin ta kara yi, ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya fa yayi yunkuri ya
dawo na daya a Nahiyar Afrika wato gaba da kasar Afrika ta Kudu da Kasar
Algeria. Suka ce arzikin Najeriya ta hau zuwa dalar amurka biliyan dari hudu da
sha biyar da digo takwas. Ita kuma Afrika ta Kudu dala biliyan dari biyu da
tamanin da digo uku na kudin amurka, itama kasar Algeria dalar amurka biliyan
dari daya da sittin da takwas da digo uku. Duk da cewa ita hukumar kula da bada
lamuni ta kasa wato IMF ta nuna cewa tattalin arziki na duniya gaba daya yana
fuskantar barazana na rashin cigaba na azo a gani.
Ita ma hukumar da take auna ingancin
tattalin arzikin kasa ta FITCH Ratings tace Tattalin Arzikin Najeriya zata samu
walwala a shekara ta 2017, domin tace tattalin arzikin Najeriya zai girma da
kashi biyu da digo shidda 2.6% bayan halin kunci da ta samu kanta a shekara ta
dubu biyu da shashidda 2016 da kashi daya da digo biyar wato 1.5%. ita dai
wannan hukumar tayi bayani cewa tsarin darajar musayar kudi da babban bankin Najeriya
ta kawo ta taimaka wajen canjin alkalumar sannan kuma kudinda ake sa ran Gwamnatin
Tarayya ta kasha wajen manyan ayyuka a kasar idan ya yiyu zai matukar taimakawa
wajen gyara tattalin arzikin kasan Najeriya.
Duk da abinda wannan cibiyoyin suka ce, wasu dai ‘yan Najeriya sunce fa
wannan cangin alkalumar ba zai rasa nasaba da gagarumar noman da akayi wannan
shekarar ba, wanda masu lura sukace an dauki shekaru masu yawa robon da ai irin
wannan noman na ba kama hannun yaro. Kuma da haka ne masu lura da tattalin
arziki suke cewa lallai fa ‘yan Najeriya sai sun kara hakuri sosai sun maida
hankali kan noma da kayayyakin da ake kera su a Najeriya, cewa hakan shine fa
zai ceto kasar daga cikin halin da take ciki na rashin aikin yi da rashin samun
kudin shiga ga gwamnati.
Ahmad Mati ya rubuta wannan
Yana shafin Twitter: @ahmadmati1
No comments:
Post a Comment