An kashe wani mutumi don yayi fitsari kusa da Coci
– ‘Yan Sandan Kasar Jamus sun tabbatar da cewa an kashe wani mutum har lahira don kawai yayi fitsari kusa da wani Coci
– Wasu mutane hudu suka kama wannan mutumi da duka, har aka yayi sanadiyar rasa ran sa
– Wannan abu ya faru ne a Garin Freiburg Kudancin Jamus
‘Yan Sandan Kasar Jamus sun
tabbatar da cewa an kashe wani mutumi har lahira don kawai yayi fitsari kusa da
wani Cocin Katolika a Garin Freiburg da ke Kudancin Jamus. Wasu mutane guda
hudu dai suka kama wannan mutumi da duka har aka yi sanadiyar rasa ran sa don
kawai yayi bawali kusa da wani Coci a Ranar Alhamis ta Jiya.
Wadannan mutane sun shiga
zagin wannan mutumi yayin da ya zo zai yi fitsarin, daga baya kuma suka rufe sa
da shegen duka har suka ga bayan sa. Wannan mutumi dai tsoho ne, mai shekaru
kimanin 51.
Yanzu haka dai ‘Yan sandan
Birnin Freiburg sun bazama neman wadannan mutane da suka aikata wannan laifi.
Wannan abu dai ya faru ne a Jiya Alhamis, a Garin Freiburg da ke can Kudancin
Kasar, mafi yawan mutanen Garin dai Mabiya Cocin Katolika ne.
A Kasar Jamus dai fitsari a
waje, musamman ginin Coci, babban laifi ne, ana zargin bawalin da ake yawan yi
ke sa wasu gine-ginen suna rushewa, Hukuma ta kan dauki mataki mai tsananin ga
mutanen da aka kama suna fitsari a waje.
[NAN]
Twitter: @Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment