An kusa fara bikin cika shekaru goma da hawan Sarkin Musulmi
– Gwamnatin Jihar Sokoto za ta yi bikin cika Shekara goma da nada Alhaji Sa’ad Abubakar Sarkin Musulmi
– An nada Mai girma Sa’ad Abubakar III Sarkin Musulmi bayan rasuwar Muhammadu Maccido
A cikin watan Nuwamban nan mai zuwa ne za a cika shekaru
goma daidai da nada Mai Girma Alhaji Sa’ad Abubakar III a matsayin
Sultan na Sokoto, watau Sarkin Musulmi. Kwamishinan labarai na Jihar Sokoto,
Danladi Bako ya bayyana haka a yau, Inji Jaridar DailyTrust.
Za a gudanar da wani taro na
Ilmi a ranar cika shekara goma na Sarkin, inda za a kaddamar da wani littafi
game da rayuwar Sarakun Musulmi. Littafin zai yi magana ne game da gudumuwar
Sarakunan Musulmai wajen tattalin arzikin Kasa da kuma Siyasar al’umma da mulki
a yankin na Sahel.
Kwamishinan labarai na Jihar
Sokoto, Danladi Bako wanda shine ke rike da Sarautar Kogunan Sokoto, kuma yana
cikin wadanda za su gudanar da wannan taro, yace za ayi taron ne a Ranar 2 ga
watan Nuwamban gobe. Bako yace za a gayyaci manyan masana na duniya zuwa wannan
taro.
Alhaji Danladi Bako yace za
a duba binciken su Shehu Danfodio da kuma dan sa Abdullahi na Gwandu dsr, yace
a bakin na Sarkin Musulmi za kuma ayi hawan Durbar. An nada Mai Girma Alhaji Sa’ad Abubakar III
a matsayin Sultan na Sokoto, watau Sarkin Musulmi a shekarar 2006.
Allah ya ja zamani.
Twitter: @Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment