Obanikoro ya jefa Fayose cikin matsala
– Musliu Obanikoro ya fasa kwan yadda ya raba N4.7b da ake zargi
– Sai dai yace an raba wannan kudi ne domin kawar da Kungiyar Boko Haram daga Legas
– Obanikoro yace ta jirgin sama aka tura kudin
Kamar dai yadda aka sani
Tsohon Karamin Ministan tsaro lokacin Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan,
Musliu Obanikoro ya dawo Najeriya, inda har ya sallama kan sa ga Hukumar EFCC.
Sai dai Tsohon Ministan, Musliu Obanikoro ya jefa Gwamna Fayose na Jihar Ekiti
cikin babbar matsala.
Ana zargin Musliu Obanikoro da shan kwana da
wasu kudi da suka kai Biliyan hudu da miliyan dari bakwai da hamsin da biyar ta
wani Kamfanin sa mai suna Slyva Mcnamara. Wadannan kudi dai sun fito ne daga
Ofishin mai bada shawara kan harkar tsaro ONSA a lokacin. Sai dai Obanikoro yace
an raba wannan kudi ne domin yakar da ‘Yan Kungiyar Boko Haram da ke Jihar
Legas
Musliu Obanikoro yace ya
turawa Ayo Fayose Naira Biliyan biyu da miliyan dari biyu da ashirin da uku da
kuma wasu Biliyan daya da miliyan dari uku cikin kudin ta hannun wani wai shi
Mista Abiodu Agbele. An dai tura wannan kudi ne ta jirgin sama.
Wadannan kudi dai duk suna
cikin Dala Biliyan biyun da aka yi awon gaba da su daga Ofishin ONSA na Kasa,
watau mai bada shawara kan harkar tsaro, Sambo Dasuki, a lokacin. Wadannan kudi
dai asali na sayan makamai ne.
Muhammad Malumfashi
Twitter: @Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment