‘Yan Sanda sun kama wata mata ta saye jinjiri dan wata biyu
– Jami’an ‘Yan Sanda sun kama wata Tsohuwa ta saye jinjirin wata biyu da haihuwa
– Yanzu haka Miss Ross Edward na nan a tsare wajen Hukuma
– Uwar wannan Jinjiri ta sayar da shi N450, 000 saboda talauci
Jami’an ‘Yan Sanda sun kama
wata mata mai suna Miss Ross Edward dauke da jinjiri dan wata biyu. Wannan mata
ta bayyanawa Jami’an ‘Yan Sanda cewa ta saye wannan jinjiri ne daga hannun
mahaifiyar sa kan kudi N450, 000
Cordelia Mani Nwanwe,
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Akwa-Ibom, ya tabbatar da faruwar wannan abu, ya kara
da cewa akwai wani likita mai suna Dakta Eneyo Nyang da aka hada kai da shi
wajen sayar da wannan jinjiri. Jami’in ‘Yan Sandan na Jihar yace za su cigaba
dayin iyaka kokarin su wajen aikin kare rayuwkar jama’a a Jihar.
Mahaifiyar wannan jinjiri
tace babu ce ta sa ta sayar da diyar da ta haifa, uwar jinjirin Miss Comfort
Effiong tace ba ta da kowa; uwar ta tana fama da rashin lafiya, sannan kuma
mijinta ya rasu. Wannan mata tace ta rasa yadda za tayi a duniya, hakan ta sa
ta sayar da jinjiri dan wata biyu domin samun kudi.
Wannan mata watau Miss Ross
Edward tace tana da sha’war da, shiyasa ta saye wani jinjiri. Mahaifiyar
jinjiri tace dai ba ta da wanda zai kula da yaron ko ya zauna hannun ta,
shiyasa ta sayar N450000.
No comments:
Post a Comment