Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar-Lemu
Kudirin daidaita Rabon Gado: Sheikh Umar Sani Rijiyar-Lemu ya ja kunnen Sanatocin Najeriya
– Wani Babban Malami a Kasar nan ya ja kunnen Sanatocin Najeriya game da kudirin rabon gado
– Dr. Muhammad Sani Rijiyar-Lemu ya gargadi Sanatoci game da yunkurin raba kason gadon maza daidai da mata
– Malamin yace wannan ya sabawa addinin musulunci kuma tsokanar fada ce
Wani Babban Malamin Musulunci Sheikh Muhammad Sani
Umar Rijiyar-Lemu ya gargadi Sanatocin Najeriya game da yunkurin kawo wata doka da za ta sa
rabon gadon namiji ya zama daidai da na diya mace a Kasar nan. Wata Sanata mai
suna Abiodun Olujimi daga Ekiti ta kawo wannan kudiri.
Sanata Misis Biodun Olujimi ta kawo kudirin daidaita kason namiji da mace a Majalisa
Babban malamin da ke Kano yace wannan doka ta sabawa Addinin
musulunci, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar-Lemu yace akwai yi wa Addinin
Musulunci Karen-tsaye da kuma tsogala a wannan kudiri.
Malamin yace akwai yadda
shari’a ta tsara rabon gado a addini cikin Hikima kuma babu yadda za ayi a
canza wannan. Asali ma duk musulmin da ya musanya hakan, yayi ridda daga musulunci, don kuwa yayi fito-na-fito da Shari'ar Allah. Dakta Rijiyar-Lemu ya kira
Sanatocin Najeriya musamman wanda suke Musulami da ke Majalisar da su guji amincewa da wannan kudiri.
Tun a ranar farko dai wani Sanata Kirista mai suna Emmanuel Bwacha yace hakan
ya saba addinin Kiristanci, inda ya janyo nassoshi daga Littafin sa.
A baya wani Shehin Malami a Kasar nan , Dahiru
Bauchi yayi kira ga Sanatocin Kasar da su bi a sannu game da abubuwan da suka
shafi addini a Kasar. Sheikh Dahiru Bauchi yace musulunci ya tsara ka’idar
rabon gado a Kur’ani.
Haka ma Kungiyar Izala watau JIBWIS karkashin Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ma dai tace wannan kudiri ya sabawa shari'ar Musulunci.
A musulunci dai namiji na karbar kashi biyun na mace a wasu yanayin, saboda kuwa a ko yaushe, da namiji shi yake kula da mace.
Muhammad Malumfashi daga Zariya
@Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment