Yadda aka kama mutumin da ya saci Yarinya Sultaana a Kaduna
Muhammad Malumfashi: Na kawo rahoton yadda aka kama wani mutumi ya sace wata yarinya Sultaana. A wannan
karo na kawo maku cikakken labarin yadda wannan abu ya auku bayan mun yi
magana da iyayen wannan yarinya ta wayar Tarho.
An sace wannan yarinya Sultana
watau Zainab Umar watanni bakwai da suka wuce. Da yake abin da rabo sai ga shi
an gan ta a karshen wannan mako. An sace Sultaana ne a Badiko yayin da za ta je
Makarantar Islamiyya. Bayan dai har iyaye sun saduda, an fawwalawa Ubangiji, kwatsam
sai ga Sultaana ta dawo.
Masha Allah. Sultaana ta dawo
Bayan
an sace ta daga Badiko, an yi kokarin canza mata unguwa zuwa Malali, a can kuwa
wata rana ‘Yar uwar iyayen yarinya suka hadu da matar da ta ke dauke da su.
Abin ya faru ne lokacin wannan mata tana cikin Keke Napep, kawai sai ta
hango Sultaana, nan take, tace da mai babur ya hanzarta wajen wancan mata. Sai
ga mata Inyamura da yaran hausawa har biyu suna tafiya, nan kuwa mata tace ai
wannan diyar mu ce da aka sace. Inyamura tace Allan-barin ‘Ya ‘yan ta ne- ‘Na my pikin’ domin ba ta ko jin Hausa. Nan fa mata ta tara Jama’a, har ta kai
tace idan ana so a gane, a duba hannun yarinya inda ta taba konewa, ana dubawa,
sai ga shaida kuwa, daga nan sai wajen ‘Yan sanda kaya-kaya.
AlhamdulilLahi. Sultaan da Goggon ta
Ko
da aka je ga Hukuma sai mijin wannan mata wanda asalin sa mutumin Yola ne, ya
bayyana cewa hakikanin gaskiya, ba diyar su bace. Ya ji tsoron idan ya fada a
waje, za a masa illa. Wannan mutumi ya bayyana cewa shi dai yana da sha’awar
yara mata, tun da bai haifa ba, sai ya ga Sultaana wata rana ya dauke ta. Har
kuwa ya sa ta a makaranta, ana kuma mata darasi a gida, ya saya mata kayan
wasa, har da wani keke na kusan dala dubu, ga lalle ta sha rangadau. Shi kuma
Nasir-wanda har an sauya masa suna zuwa Ibrahim, wani yaro ne da ya sato shi
ma, mahaifin sa kuma yaron Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Namadi Sambo ne.
A
gidan wannan mutumi dai an samu wasu yaran manya masu kimanin shekaru 16; akwai
mai koyawa yara-Su Sultaana karatu, akwai mai gadi da kuma wani mai
aikace-aikace. Tuni dai har wannan mutumi yayi wa yaran nan Fasfo na Kasar
waje, yace kuma sana’ar sa kasuwanci daga Dubai zuwa Najeriya. Matar sa kuma
Inyamura, yace ta musulunta ne. Tuni dai har Gwamnan Jihar Malam Nasiru El
Rufai ya leka wurin.

Mai Girma Gwamnan Kaduna Mal. Elrufai tare da su Sultaan da Nasir, takwaran sa. Ko da yake an canza masa suna
Muhammad Malumfashi ya rubuta wannan labari daga Kaduna. Na buga wannan labari a shafin NAIJ Hausa.
Sai a bincika: Shafin nawa na NAIJ Hausa
A iya biyo ni shafin twitter ta lambar @ya_waliyyi.
No comments:
Post a Comment