– Wani dan Kungiya shan jini da aka kama ya bayyana abin da ya shiga cikin Kungiyar
– Yace jarin kasuwanci yake nema shiyasa ya shiga wannan Kungiya
– Yanzu haka ‘Yan Sanda sun kama wannan mutumi
Jami’an ‘Yan Sanda sun kama
mutane 12 da ake zargi ‘Yan Kungiyar Shan jini ne a Unguwar Apo da ke Birnin
Abuja. An kama wadanna mutane da bindigogi, da adda da wukake Inji Jaridar
Punch. Ana zargin wadannan mutane suna cikin wata Kungiyar shan jini mai suna Norsemen.
Kowane daga cikin wadanda
aka kama ya bayyana dalilin da ya sa ya shiga wannan Kungiyar shan jini. Wani
daga cikin su mai suna Fidelis Ogabor yace ya shiga Kungiyar shan jini ne domin
karbar bashin kudi, Mista Ogabor yace yana neman kudi N200, 000 ne domin ya
bude shagon gyaran gashi.
Mista Ogabor yace an kore sa
ne daga wurin aiki, hakan ta sa ya shiga wannan Kungiyar shan jinni. Bayan ya
nemi taimakon kudi daga wani Mista Williams, sai yace masa sai da ya shiga
Kungiyar shan jini na Norsemen idan
yana bukatar a taimaka masa.
Fidelis Ogabor yace ya samu
aron kudin bayan ya shiga Kungiyar shan jini, sai dai da ya gaza biyan bashin,
‘Yan Kungiyar shan jini sun tura ‘yan iskan gari suka likida masa dan-karan
duka. Bayan nan ne ‘Yan Sanda suka kama sa, aka ce yana cikin ‘Yan Kungiyar
shan jini.
No comments:
Post a Comment