Sunday, October 2, 2016

Shugaba Buhari: Jiya ba yau ba



Shugaba Buhari: Damukaradiyya da Mulkin Soja

Shugaba Muhammadu Buhari ya mulki Kasar nan a lokacin Soji daga Disamban 1983 zuwa Agustan shekarar 1985. A ranar 29 ga watan Mayun bara kuwa ya kara darewa mulkin Kasar, a matsayin Shugaba na 15 a Najeriya, sai dai a wannan karo, mulkin farar hula. Wanda hakan ta sa ya zama mutum na farko bayan Obasanjo da ya mulki Kasar sau biyu; a karo na Soji da Damukaradiyya.
Sanannen abu ne cewa Shugaba Buhari ya dade yana neman takarar Shugabancin Kasar nan, har yayi ya gaji. Har sai shekarar 2015, inda ya samu sa’ar buge Tsohon Shugaba Jonathan Goodluck. Mutane da dama dai ba su yi amanna da Buhari ba saboda suna ganin cewa, Soja kowa ya tube kaya, yana gida, Soja ne. Duk da cewa ya sha jaddada riddar sa gaban duniya, ya zama dan siyasa na damukaradiyya; tun bayan kifewar Daular Tarayyar Kasar Russia. Wasu dai suna ganin anya wannan Janar din zai fasa halin sa-na Soja idan ya samu mulki?
Duk da cewa wani zai iya ce maka ai tuwo ba ya taba canza suna. Ko a yanzu a mulkin Shugaba Buhari an zarge sa da karya hakkin bil adama, kamar yadda ya kama Sambo Dasuki, Nnamdi Kanu da Ibrahim Zakzaky ya garkame. Ga shi ya rufe hanyoyin shiga na ‘border’ kamar yadda dai yayi a baya, ga wani tsarin kasuwanci da yake kokarin  kullawa da Kasar China, dsr dai. Ga kuma yunwar Buhariyyah, ta dawo…Sai dai mun kawo maku irin bambancin da aka samu tsakanin zuwan Shugaba Buharin na farko da kuma na yanzu: 
Cire tallafin man fetur ‘Subsidy’
Babu irin matsin da Shugaba Buhari bai sha ba a shekarun 84-85 na ya cire tallafin man fetur, da na sauran kayayyaki; Sai dai Janar din ya hau kujerar na-ki, yace sam ba zai yi hakan ba, don talakawa. Sai ga shi abin mamaki, wannan karon ya cire tallafin man fetur din. Ko a zamanin Shugaba Jonathan, Buhari bai amince da cire tallafin ba. Wannan karan kuwa, dara ta ci gida, sai dai ‘Yan Najeriya ba su yi masa bore ba. A baya dai Najeriya ta saba biyan kudi da ya kan wuce Naira Tiriliyan guda kan tallafi, mafi yawa kuma ana tunanin aljihun bogi yake zarcewa. Yanzu dai man fetur din da Najeriya ta ke sha ya ragu, da alamar tambaya. 
Karya farashin dala ‘Devaluation’
Haka dai a wancan lokaci, cikin sharuddan da Kungiyar IMF ta ba sa, akwai karya farashin kudin Naira, nan ma Janar Buhari yace ‘Ina’ Kamar dai batun ‘Subsidy’, Bankin CBN na Kasar ya saki farashin kudin Nairar a sama yana lilo-inda kasuwa ta kada da shi, ba dai kamar yadda Shugaba Buhari ya so ba. Farkon hawan mulkin sa, yayi kokarin tokare darajar Nairar da ‘Yan dalar da Kasar ta ke da su, sai dai aikin ya wuce nan.
Majalisa
Aiki da Majalisa bakon abu ne wajen Shugaba Janar Buhari, ya kuwa yayi iya bakin gwargwado. Tun fari, Shugaba Buhari yace ba zai tsoma baki cikin sha’anin zabenMajalisun Kasar ba, yin hakan dai ya zo da irin na sa cikas din. Ba kamar yadda yayi a baya ba, sai dai kawai Fadar Koli ko na Tarayya na Soji ‘Supreme Military Council’ da ‘Federal Military Council’ ta murza gashin baki, tace ga yadda za ayi. Asali ma dai Shugaban na da kudurori da dama gaban Majalisar, tun bara wanda sun ki cewa ko ‘hmm’, wasu kuma na tafe, ko ya za a kaya? Ko dai fita Kasar waje Shugaban Kasar zai yi, sai ya rubutawa Majalisar takarda. Ga batun kasafin kudi da aka yi ta fadi-tashi.
Neman hana ‘yan jarida Magana
A shekarar 1984, Shugaba Buhari ya kirkiro wata Doka mai lamba 4, wanda tace duk dan jaridar da ya rubuta karya game da Gwamnati, zai sha dauri ko tara na kudi. Hakan ta sa aka daure wasu ‘yan jarida a Kasar, a bara wani Sanatan majalisar Dattawa na Kasar nan, ya nemi ya kawo irin wannan kudiri a Majalisa, sai dai tuni Shugaba Buhari yace wannan ba da shi ba. 
Ministoci
Dole wannan karo Shugaba Buhari ya bi kundin tsarin mulkin Kasa wajen nada Ministoci, bayan dogon lokaci, ya nada Ministoci; guda daya daga kowace Jiha. Ba kuwa haka aka saba a mulkin Soji ba, ka iya ganin wata Jiha ba ta da wakili a Majalisar zartarwar. Sai dai Buhari ya nada kan sa a matsayin Ministan man fetur, ko can dai ya rike irin wannan matsayi a baya kafin ya zama Shugaban Kasa.
Matar Shugaban Kasa
A wancan karo ba a san Matar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba sosai-Hajiya Safinatu. A bara kuwa wajen yakin neman zabe, ‘Yan Najeriya sun ga Aisha Buhari-Matar Muhammadu Buhari. Ta kuwa yi alkawari kamar na mai gidan ta, cewa ba za ta kama Ofis ba na ‘Uwargidan Najeriya’ kamar yadda aka saba don ya saba dokar Kasa. Sai ga shi yanzu ta kan je har Amurka, har da mai mata kwaliyya, amma a matsayin ‘Wife of the President’ ba kuwa ‘First lady’ ba, watau Matar Shugaban Kasa, ba Uwargidan sa ba. To ai an ki cin biri, an ci dila.
Kasafin Kudi da Ayyukan Kasa…
Bayan hanbarar da Gwamnatin Shehu Shagari, Buhari ya rage kasafin kudin Kasar na shekarar da ta biyo, sai dai wannan karo, Shugaba Buhari ya ma kara karfin kasafin Kudin Kasar Najeriya ne a wannan shekarar, daga Tiriliyan hudu da rabi zuwa fiye da Tiriliyan shida.
Kamar dai yadda ya kara karfin kasafin kudin Kasar nan, Shugaba Buhari ya kara yawan kudin da aka ware na ayyuka-irin su tituna, gada, gidaje dsr. Shugaban Kasar ya ware kusan rabin Tiriliyan wajen wannan, ba ma za a hada da abin da Gwamnatocin baya suka saba ba. A shekarun Soji kuwa, Buhari tsaida duk wasu manyan ayyuka da Shagari ya fara, da cewar babu kudi. Haka kuma akwai shirin daukar ma’aikata da dama har sama da 500000, a mulkin Soji kuwa, Janar Buhari yayi sanadiyyar rasa aikin mutane dubunnai.
Bindige ‘yan kwaya
A lokacin Soji, Janar Buhari ya harbe wadanda aka kama da laifin safarar kwayoyi har lahira, mace da namiji, babba da yaro. A wani kaulin, wannan na daga cikn dalilin da ya sa aka kifar da Gwamnatin sa. Sai dai wannan karo babu wata doka mai kama da wancan mai lamba ta 20. Amma dai, ‘Yan Kwastam da Ma’aikatan hanyoyin ruwa sun rufe shigo da kayan jabu. 
Rancen kudi wajen Gwamnatin Jihohi
A lokacin mulkin Soji, Buhari ya haramtawa masu rike da Jihohin Kasar cin bashi ko ta wani iri. Kamar dai yadda ya karbi (ko ace ya kwata) mulkin Kasar daga hannun Shagari, Gwamnoni da dama sun gaza biyan albashin Ma’ikatan su, a mulkin Tsohon Shugaba Jonathan. Gwamnatin Buhari ta bada aron kudi domin a biya ma’aikatan Jihohi, kwanan nan ma kum, Gwamantin Tarayya ta kara fito da wani sabon tsarin rancen ga Gwamnatin Jihohin Kasar.
Yaki da Cin Hanci da Rashawa
Har yanzu dai babban dodon da Shugaba Buhari yake fada da shi, shi ne Rashawa a Najeriya. Ko da dai bai sauka daga wannan matsayin ba, sai dai salon ya canza. A zamanin Soji, ya kama ‘yan siyasa da dama ya daure, sai dai kowa tashi ta fishe shi. Yanzu kuwa, tsarin mulkin Kasa yace barawon da ba a kama ba, sunan sa Muhammadu ba kamar da can da Buhari ya rika amfani da tsarin ‘Na shiga ban dauka ba... ba ta fitar da barawo’ ba. Da bakin sa yace yanzu sai ya ga wadanda suka shiga Gwamnati a cikin manyan motoci, amma tsarin mulki yace har sai an kama su da laifi baro-baro. Ba don haka ba da tuni an maimaita na Ummaru Dikko da Deziani Madukwe.

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...