Monday, October 10, 2016

Ko ka ga mutumin da yafi kowa laifi a duniya?



Yau ga Mutumin da aka daure fiye da sau dubu



  • Yayin da wasu ke tsoron su aikata laifi, ga wani nan ya aikata laifuffuka ya fi a kirga a duniya

  • An kama wannan ta’aliki fiye da sau dubu a rayuwar sa

  • Duk shi kadai, an daure shi sau kusan 1300




 
Yayin da wasu ke tsoron su aikata laifi, ga wani nan ya aikata laifuffuka ya fi a kirga a duniya. Watakila ba ka taba jin wannan gogan mai suna Henry Earl ba? Wannan mutumin ya fi kowa shan kamu a duk duniya.

Henry Earl ko kuma kace masa James Brown ya shiga Tarihin duniya, inda ya zama wanda ya fi kowa shan dauri a duniya. Sau kusan 1300 Hukuma tana kama wannan mutumi a rayuwar sa. Ko ka taba jin wani namji a duniya irin sa?


Yanzu haka James Brown ya kai shekaru 66 a duniya, ya kuma fara shiga gidan yari ne a shekarar 1970, watau kusan shekaru hamsin da suka wuce. A wancan lokaci Henry Earl yana dan matashi mai shekaru 20 rak a duniya da haihuwa. An dai saba kama Henry tun wancan lokacin da laifin maye a cikin Jama’a, daukar makami da dai sauran su.

Henry Earl mutumin Lexington ne, na Kentucky ta Amurka. Wannan mutumin masifaffen mashayin giya ne dai a duniya. James Brown dai ya zauna a gidan yari na kwanaki fiye da 6000 a rayuwar sa ta duniya. A shekarar 2003 yayi kaurin suna a duniya bayan Gidan CNN ta fito da shi. Watakila Har ma dai ya saba da gidan kaso.


Source: NAIJ.com

Muhammad Malumfashi, Twitter: @Ya_waliyyi

1 comment:

  1. Ikon Allah, to amma shi wannan mutumin ya na kuwa da aure?
    ba ya tunanin halin da iyalan shi da 'ya'yan shi za su shiga ko ma in ce suke ciki?

    ReplyDelete

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...